Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazak, ya bukaci kwararrun masana tattalin arzikin kasa da su taimaka wajen lalubo hanyoyin da za a dakike hakar ma’adinai ba bisa ba da ke kara dagula lamuran tsaro a fadin kasar nan.
Gwamnan ya yi rokon ne a wajen bude babban taron kwararrun masana tattalin arzikin kasa karo na uku da ya gudana a dakin taron jami’ar Al-Hikmah da ke Ilorin, babban birnin jihar.
- Ba Zan Goyi Bayan Ƙudirin Ƙarin Haraji Ga Talakawa Ba – Sanata Ndume
- Sin Ta Zargi EU Da Bayar Da Kariyar Cinikayya Bayan Da Kungiyar Ta Kakaba Karin Haraji Kan Motoci Masu Aiki Da Lantarki Kirar Sin
AbdulRazak, wanda ya samu wakilcin kwamishinan ma’adinai da albarkatun kasa na jihar, Dakta Afees Abolore, ya misalta halin da ake ciki na yawaitar masu hakar ma’adinai ta barauniyar hanya da cewa akwai bukatar daukan matakin gaggawa.
Kazalika, gwamnan ya nemi masanan da su yi amfani da taron wajen ganin sun bullo da tattauna yadda za a samu kyautata harkokin hakar ma’adinai da kuma shawo kan matsalolin da suke bangaren.
“Albarkatun kasa na kan gaba wajen farfado da tattalin arzikin kasa nan.”
AbdulRazak.Ya ce gwamnatin tarayya za ta iya sanya bangaren albarkatun kasa a matsayin hanya na gaba-gaba wajen samar da kudaden shiga da kuma samar wa matasa ayyukan yi, sai dai abun takaici masu hakar ma’adinai ta barauniyar hanyoyi sun mamaye sashin da kuma kara janyo barazanar tsaro.
Gwamnan ya ce, gwamnatin Kwara a shirye take wajen hada hannu da masu zuba jari a ciki da waje kan wannan bangaren da ma sauran bangarorin kyautata tattalin arziki. Ya kuma ce Kwara ta kasance jiha mai saukin hulda da masu zuba hannun jari a bangaren gudanar da kasuwanci.
Tun da farko, shugaban NSEG, Dakta AbdulRazak Garba, ya ce, lokacin ya yi da Nijeriya za ta maida wajen kula da albarkatun kasarsa da kyautata muhalli.
Garba, wanda ya ce bangaren albarkatun kasa na da gagarumar rawar takawa a cikin kasar nan, ya lura da cewa bangaren na bukatar jerin kalubale.
Ya jero wasu daga cikin kalubalen da suka hada da rikitattun tsarin mulki, gazawar ababen morewa, gibin kudi, bukatar daidaita cigaban fasaha da dai sauransu.