Alkalin Babban Kotun Tarayya da ke Abuja, Mai shari’a Obiora Egwuatu, ya bayar da belin matasa 67 daga cikin 76 da aka gurfanar kan zanga-zangar #EndBadGovernance da aka yi a watan Agustan 2024.Â
An bayar da belin kowane daga cikinsu a kan kudi Naira miliyan 10.
- Matsalar Almajirai Da Yaran Da Ba Su Zuwa Makaranta Kalubale Ga Shugabannin Arewa – Sultan
- Ba Mu Karɓi Kuɗin IPMAN Ba Bare Mu Hana Su Mai – Matatar Dangote
Matasan wadanda shekarunsu ba su wuce shekaru 15 ba, za su gabatar da mutum guda daya a matsayin mai tsaya musu, kuma dole ne ya kasance ma’aikacin gwamnati.
Kazalika, an gurfanar da manya 87 wadanda suka gudanar da zanga-zanga kan irin wannan laifin.
Tun da farko, LEADERSHIP Hausa ta ruwaito cewa wasu daga cikin matasan, wadanda shekarunsu ke tsakanin 12 zuwa 15, sun suma saboda tsananin yunwa yayin da ake zaman kotun a ranar Jumma’a.
Karin bayani na tafe…