Ma’aikatan kiwon lafiya ta Jihar Nasarawa ta gudanar da gangamin wayar da kan al’umman jihar game da cutar hanta.
Tawagar malaman jinya ta gayyaci al’umma don tunawa da ranar cutar hanta ta duniya ta shekarar 2022 wato ‘World Hepatitis Day 2022 Pop-Up’.
- Goron Juma’a
- Kotu Ta Umarci Wani Ma’aikacin Gwamanti Da Ya Dawo Da Albashinsa Na Shekara 11 A Filato
Da yake jawabi ga manema labarai dangane da mahimmancin zuwa gwajin kwayan cutar hanta, kwamishinan kiwon lafiya na Jihar Nasarawa, Dakta Ahmad Baba Yaya, ya yi kira ga al’umman jihar da su rika zuwa gwajin kwayar cutar domin kare kawunansu daga yaduwar cutar a cikin al’umman.
Kwamishinan ya gargadi al’umman jihar da su daina ta’ammuli da wurare mara tsafta, domin ana iya kamuwa da cututtuka ciki har da na hanta a wuraren da babu tsafta.
Ya ce cutar hanta ta kasu kashi biyar, inda ya ce daga cikin cutar akwai wanda ake iyayi masa rigakafi, akwai kuma wanda ba a yi masa rigakafi idan an kamu da shi sai dai a yi ta shan magani, sannan akwai wanda ake warkewa idan an sha magani, akwai kuma wanda baya warkewa sai dai cutan ba zai yi tasiri a jikin mutum ba idan ana shan magani.
Ya kara da cawa ana iya daukar cutan ta hanyoyin gamayyan haduwan jinni, amma ba a iya daukar cutan ta hanyoyin runguman juna ko ta hanyan zufa kamar yadda wasu ke cewa. Ya ce jariri yakan iya daukar cutan a cikin mahaifiyarsa.