Shugaban Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS), CGI Isah Jere Idris, ya amince da sauya wuraren aiki ga manyan jami’ai 69 zuwa manyan ofisoshin hukumar na shiyyoyi da jihohi da ke sassan kasar nan.
Sanarwar da ta fito daga Jami’in hulda da jama’a na hukumar, ACI Amos Okpu ta bayyana cewa daga cikin adadin jami’an da aka sauya wa wuraren aikin akwai masu mukaman Kananan Mataimakan Kwanturola Janar (ACG) guda takwas sai masu mukaman Kwanturololi (CIS) guda 61 da aka rarraba su a sassan manyan ofisoshin hukumar.
- Hukumar Kwastom Ta Cafke Miyagun Kwayoyi Na Kimanin Biliyan N1.4 A Legas
- Hukumar NDLEA Ta Kona 560,068kg Na Hodar Iblis Da Wasu Kwayoyi A Legas
Cikin masu mukaman ACG da aka sauya wa wuraren aikin akwai ACG KM Amao wanda a da yake Kwanturolan Jihar Ogun amma yanzu an maida shi Sashen Ayyuka Na Gaba Daya a shalkwatar hukumar da ke Abuja, sa’ilin da ACG KN Nandap wanda a baya yake kula da Babban Filin Jiragen Sama na Murtala Mohammed da ke Legas a yanzu kuma aka sauya masa zuwa Sashen Bayar da Takardu ga Bakin Waje (CERPAC) a shalkwata.
Har ila yau, ACG Abdullahi M Usman a yanzu shi ne Shugaban Sashen Kula da Shige da Fice na Yau da Kullum a shalkwatar hukumar, yayin da ACG BN Alawode ya zama Shugaban Sashen Kula da Walwala da Daidaiton Jinsi, sai kuma ACG EC Esedo da aka mayar zuwa Ofishin Shiyya ta hudu da ke Minna.
Shi kuwa ACG MA Ushie na Sashen Yaki da Damfara an mayar da shi zuwa Sashen Difilomasiyya da Fasfo, sai ACG ES Fagbamigba wanda a da yake kula da Babban ofishin Iyaka na Idi-Iroko da aka tura ya zama shugaban kula da iyakokin kasa na kan-tudu a shalkwata.
Daga cikin masu mukaman Kwanturololi da aka sauya wa wuraren aikin kuwa akwai Compt. AO Adesokan da aka mayar zuwa Babban Filin Jiragen Sama na Murtala Mohammed da ke Legas daga Sashen Horaswa da Inganta Kwazon Ma’aikata, yayin da mukaddashin babban jami’in ofoshin Kwanturola Janar, Compt. Ahmed Mustapha ya zama sabon Kwanturolan Kano.
Sauran sun hada da Compt. Shittu Olajire Fatai wanda a yanzu aka mayar da shi Ofishin Kula da Iyaka na Legas; da Compt. Gwama Muhammad wanda a yanzu shi aka ba shugabancin Ofishin kula da iyaka na Idi-Iroko; da Compt. MM Saddik wanda a yanzu aka ba shi matsayin Babban Jami’in Ofishin Kwanturola Janar.
Shi kuwa Compt. AO Bewaji an mayar da shi ne zuwa shalkwatar hukumar yayin da Compt. Michael Dike ya karbi ragama a matsayin Kwanturolan Iyaka na Seme da ke Legas. Shi kuwa Kwanturola mai kula da da’ar aiki an tura shi ya shugabanci yankin Jihar Osun yayin da Compt.
Sabo A Rano da ya kasance Kwamandan Makarantar Horas da Jami’ai ta Kano aka mayar da shi zuwa Jihar Gombe.
Bugu da kari, Compt. FD Dakat na Sashen kula da tasoshin ruwa aka mayar da shi zuwa Jihar Akwa Ibom inda zai karbi ragama daga Compt. GE Didel wanda aka mayar zuwa sashen shige da fice a shalkwata, da dai sauransu.
Shugaban Hukumar ta NIS, Isah Jere ya hori dukkan jami’an da aka sauya wa wuraren aikin su yi amfani da basirar da Allah ya yi musu a wuraren da aka tura su wajen inganta aiki da tsaron kasa. Sauyin aikin dai ya fara aiki ne nan take.