Karuwanci na daya daga gurbatattun dabi’un da gwamnatin Neja ta haramta tun zuwan shari’ar musulunci lokacin gwamnatin Marigayi Injiniya Abdulkadir Kure, wanda ya kai gwamnatin wancan lokacin ta samar da hukuma ta musamman da za ta kula da harkokin addinin musulunci a karkashin hukuma mai kula da shari’a.
Babban aikin hukumar a lokacin shi ne, sulhu tsakanin ma’aurata, rabon gado da kulawa wajen bin dokokin shari’ar musulunci, musamman wajen tabbatar da hana shan giya da sayar da ita a bainar jama’a tare da rufe gidajen karuwai da wuraren ‘yan caca.
- Gwamnatin Gombe Ta Kafa Kwamitin Sayarwa Da Raba Takin Zamani Don Saukaka Wa Manoma
- Ma’aikatar Tsaron Sin Ta Yi Bayani Game Da Matakan Soji Da Kasar Ta Dauka
Hukumar ta yi suna wajen aiki da jajirtattun rudunar HISBA, wanda suke aiki ba dare ba rana kamar yadda majalisar dokokin jihar ta tanada, wanda dokar kasa ta ba ta dama. Ko a wancan lokacin ana karuwanci amma a fakaice, dalilin tarwatsewar karuwan zuwa gidajen haya, inda suke haduwa da abokan huldarsu a wasu kebabbun wurare ba tare sanin gwamnati ba.
Bayan wucewar gwamnatin, Injiya Abdulkadir Kure, gwamnatin Dakta Mu’azu Babangida Aliyu ta jaddada dokar hana karuwanci a jihar, amma sakamakon rashin bai wa hukumar goyon bayan da ta dace, ayyukan yaki da karuwancin ya yi sanyi, inda mafiwan karuwa suka ci gaba da tallata kawunansu a wasu manyan hanyoyi, musamman da yamma dan masu wucewa su rika daukarsu zuwa mafi akasari masaukan baki da wuraren hutuwa ba tare da an sanya masu idanu ba.
Wani lokacin kuma wasu kan labe da zawarci suna yawo a ma’aikatun gwamnati, inda su kan ziyarci wasu manyan ma’aikata da suka taka rawa a lokacin yakin neman zabe tare da ‘yan siyasa.
Gwamnatin Ma’azu Aliyu duk da ba ta ba da damar ci gaba da sakar wa karuwai mara ba, amma ba ta tsanantawa kamar lokacin gwamnatin da ta gada ba, hakan kuma bai ba da damar bude gidajen karuwai ba.
Bayan tafiyar gwamnatin Dakta Mu’azu Aliyu, gwamnatin Alhaji Abubakar Sani Bello ba ta halasta karuwancin ba, amma kuma ita din ma ba ta yi abin da ya dace wajen karfafa gwiwar hukumar ba, kasancewar ma’aikatan Hisbar ba su samu kulawar da ta dace domin ci gaba da ayyukansu.
Kasancewar hukumar shari’ar tana da bangarori da dama da suka shafi bangaren shari’a mai kula da sulhunta ma’aurata, rabon gado da bangaren yaki da giya, ya sa kusan aikin fataucin karuwan ya koma hadin gwiwa tsakanin bangaren hana sha da sayar da giya da bangaren Hisba. ‘Yan Hisban na samun damar gudanar da aikin ne da tallafin bangaren yaki da sayar da giya.
A lokata da dama bangaren ne ke taimaka wa ‘yan Hisban idan za su fita gudanar da samame.
Domin bincike ya nuna kusan duk wuraren da ake sayar da kayan barasar matan masu zamansu suna yin tururuwa a wajen, wani lokacin ma har zawara da ‘yan mata kan fake a ire-iren wadannan wuraren.
Jami’an Hisbar idan sun samu nasarar kamensu kan bai wa ‘yan sanda ne domin mika su gaban alkala. Hakan bai sanya karuwan fakewa a inda suke tsammanin gwamnatin ba ta ganin su wajen ci gaba da mummunar sana’arsu.
Binciken wakilinmu ya gano cewa har yanzu karuwan kan tsaya gefen shataletalen Sabuwar Sakatariya kusa da kofar shiga garin Minna, wasu kuma kan koma hanyar bayan gari da ya tashi daga gidajen ‘yan majalisar dokokin jiha zuwa Mararrabar masaukin baki na Aloe-bera, kasancewar akwai sabbin masaukin baki a bangaren.
Wata da ta nemi a sakaya sunanta ta ce karuwancin kama daki tsohon yayi ne, domin a kan shirya da wasu manajojin masaukan baki ta hanyar ba su lambar waya, duk wanda ya samo abokin hulda yana da kaso na abin da za a biya kafin a yi zina da su.
Wani jami’in hukumar shari’a da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce jami’an Hisbar ba cikakkun ma’aikata ba ne, ana biyan su alawus ne idan an dawo aiki, amma yanzu kusan shekaru uku kenan gwamnatin jiha ta kasa bai wa hukumar shari’a kudaden gudanar da aiki balle a samu damar gudanar da aikin yadda ya dace.
Ya ce, “Ina da tabbacin kwarewa a aikin nan, da gwamnatin jiha za ta sakar mana mara yadda ya dace ta hanyar ba mu kudaden aiki, duk wani salon karuwan nan da mun dakile shi, amma maganar kafa doka kan hana karuwanci a kan dalilan tsaro na nan daram tun ma kafin mu samu kanmu a wannan annobar ta rashin tsaro a wannan jihar.
“Kudin da ake ba mu a wannan bangaren da ya shafi biyan alawus na ‘yan Hisba da kudaden gudanar da aikin kamen a wata bai wuce dubu dari takwas zuwa miliyan daya ba, amma yanzu mun kai kusan shekaru uku gwamnati ba ta ba mu ba, kuma ba mu da wata hanyar samun kudin shiga da zai ba mu damar rike ‘yan Hisba dan gudanar da aikin.”
Koma dai mene ne, binciken da Jaridar LEADERSHIP Hausa ta gudanar kan karuwanci a Jihar Neja, ta gano cewa masu mummunar sana’ar suna amfani da wasu dubaru da salo ta hanyar fakewa da sunan neman abinci a dalilin rashin aiki da talauci.
A wasu lokutan ma har da matan auren da ke fakar idanun mazajensu, suna zuwa otel a tsakanin sallar Magriba zuwa Isha’i, wasu bayan isha’i zuwa karfe goma na dare bisa farashi dan kadan domin samun abin sanyawa aljihu.