Fili na musamman domin matasa, wanda yake bawa kowa damar tofa albarkacin bakinsa game da abin da yake ci masa tuwo a kwarya na rayuwar yau da kullum. A yau filin namu na tafe da bayanin Abba Abubakar Yakubu inda ya bayyana nasa ra’ayin game da abin da ke damunsa cikin zuciya wanda ya shafi rayuwar Aure. Ga kuma bayanin nasa kamar haka:
A makonin da suka gabata akwai wani muhimmin batu da ya dauki hankalin jama’a a zaurukan sada zumunta dangane da batun wata matashiya ‘yar gwagwarmaya Malama Layla Ali Othman wacce a wata hira da ta yi da wani shiri na tashar BBC Hausa ta bayyana halin da mata zawarawa ke fuskanta, tare da labarin irin halin da ita ma ta samu kanta a ciki bayan rabuwar aurenta da wasu mazaje. Babu shakka jama’a da dama sun yi tsokaci iri-iri a kai, gwargwadon fahimtar da suka yi wa jawabin nata. Akasari martani masu zafi ya fi fitowa ne daga bangaren maza, yayin da a gefen mata da dama suka rika tausaya mata da nuna mata goyon baya. Mai yiwuwa ko don su sun fi fahimtar karatun nata ne, a matsayinsu na mata, tunda an ce ciwon ‘ya mace na ‘ya mace ne? Amma dai kam lallai Layla ta sha raddi sosai, kodayake a irin yadda na fahimce ta, ko a jikinta. Sai dai kuma lokaci ya yi bayan an gama mayar da martani da raddi cikin fushi ko cikin raha, har da ‘yan tamore, kar a ce su ma basu ce komai ba.
- Rarara Bai Kawo Kudin Aurena Ba – Aisha Humaira
- Wasu Muhimman Abubuwa Da Ba A Sani Ba Game Da Kwakwalwa
Ya kamata kuma mu dawo mu yi karatun ta natsu, mu kalli al’amarin da idanun basira. Lallai ne duk dan halak ya so aure, saboda shi ne tushen mu, shi ne gatan mu, kuma shi ya martaba mu, ya mayar da mu masu kima da mutunci a idon duniya. Don haka ne muka ji zafi da muka ji irin maganganun da ke fitowa na sukar aure, ba don mun damu mu tsoma baki a rayuwar Layla ba, sai don aure yana cikin ginshikin rayuwar mu. Dole ne mu fito mu kare mutuncinsa. Sai dai kuma duk da haka, Hausawa na cewa, bayan tiya akwai wata caca! Bayan mun yi bambamin mun gama, ya kamata mu juyo mu kalli irin riwon da muke yi wa auren, musamman a nan Arewa, ko a tsakanin Musulmi. Mu tambayi kan mu, shin muna bai wa auren muhimmancin da ya kamata? Muna kula da hakkokin auren da ke kan mu? Yaya muke rike amanar matan da muke aura, bayan mun raba su da iyayensu da danginsu? Shin muna kula da nauyin iyalinmu yadda malamai suka ce gwargwadon hali.
Amsoshin wadannan tambayoyi su ne za su kai mu ga fahimtar abin da Layla ta tono, wato a turance ake cewa, ‘A CAN OF WORMS!’ Ban kawar da batun yahudanci ko wayewar zamani na sa wasu matan Arewa tunanin rayuwarsu za ta fi kyau idan sun yar da kwallon mangwaro sun huta da kuda ba. Amma zance na gaskiya duk macen da ka ji ta fito bainar jama’a tana gayawa duniya ta hakura da aure a rayuwarta to, ka bincika da kyau ka gani, ba a banza ba ne. Ba lallai uzurin Layla na rabuwa da mazajenta biyu na aure ya samu karbuwa a wajena ko kai ba, amma lallai mu duba a kusa da mu ba da nisa ba. Ba mu da kannai ko yayu mata, kai ko ma ‘ya’ya, (tunda mu ma yanzu mun fara aurar da na ‘yan uwa) ko wata mace a ‘yan uwanmu ko a makwafta, wadanda aure ya birkita rayuwarsu, suka fita hayyacinsu, wasu ma ciwon zuciya da hawan jini ya yi sanadin barin su duniya?
A dalilin halayen wasu mazan ne da ba su iya rikon aure ba, ko ba su kula da rikon amanar aure ba, haka take faruwa. Wani lokaci muna sane za mu rufe ido mu tilasta su komawa dakin mazajensu, ba don ba mu fahimci halin da suke ciki ba, sai don ba ma son su kashe auren su dawo gida zaman zawarci, ko ba ma son rayuwarsu ta kara shiga wani hali saboda rashin auren.
Sai dai wani lokaci mu rarrashe su, ko mu tallafa musu da wani abu da za su rage zafi ko su kama sana’a a dakunansu na aure. Kamar yadda muka tashi muka ji iyayenmu na fada ne, kuma masana zamantakewa suka tabbatar da haka. Aure dan hakuri, kuma zo mu zauna ne zo mu saba. Ko da ma’auratan da za ka ji ana cewa sun shafe tsawon shekaru suna zaune ba tare da sun rabu ko sun kashe auren su ba, idan ka yi bincike a tsanake za ka ji irin yadda suke kokarin fahimtar junansu da warware sabanin da suke samu a sirrance ba tare da barin wani ya sani ba.