Hukumar kwallon kafa ta Afrika CAF, ta fitar da jerin sunayen ‘yan wasa biyar da suka fi cancanta domin lashe kyautar gwarzon dan wasan Afrika na shekarar 2024 a hukumance, inda dan wasan Super Eagles ta Nijeriya, Ademola Lookman ya jagoranci jerin sunayen.
A wannan jadawali da hukumar ta CAF ta fitar, kyaftin din Nijeriya Wiliam Trost Ekong bai samu damar zama daga cikin sunayen yan wasan biyar ba.
- An Gudanar Da Tattaunawar Siyasa Ta Bangarorin Sin Da Amurka A Birnin Shenzhen
- Wani Dattijo Ya Mutu Bayan Ya Faɗ Rijiya A Kano
Dan kasar Cote d’Ivoire, Simon Adingra; Serhou Guirassy na Guinea; Dan wasan baya na Morocco, Achraf Hakimi, da mai tsaron gida na Afrika ta Kudu, Ronwen Williams, su ne sauran ‘yan wasa hudu da aka zaba don lashe kyautar gwarzon dan wasan CAF na bana.
Sauran nau’o’in kyaututtukan da aka sanar a ranar Litinin sun hada da Gwarzon Golan Shekara, Gwarzon Dan Wasan Kwallon Kafa na Interclub, Koci Na Shekara, Gwarzon Dan Wasa Na Shekara, Gwarzuwar Kungiya da kuma gwarzuwar tawagar kwallon kafar kasa na Shekara.
Bikin mai kayatarwa akan tsara shi domin nuna irin cigaba da harkar kwallon kafa a Afrika ta samu da kuma karrama yan wasa da kungiyoyin kwallon kafa da sukafi taka rawa a shekarar da ta gabata,wanda zai kai ga lashe kyautar gwarzon dan wasan Afirka na CAF na bana a bangaren maza da mata.