Matatar Dangote ta sanar da rage farashin man fetur (PMS) daga N990 zuwa N970 kowanne lita ga ‘yan kasuwa.
Anthony Chiejina, Shugaban Sashen Talla da Sadarwa na Rukunin kamfanonin Dangote ne ya bayyana a wata sanarwa yau Lahadi cewa; wannan matakin na nuna godiya ga ‘yan Nijeriya bisa goyon bayansu wajen tabbatar da nasarar masana’antar. Har ila yau, ya ce wannan matakin wani ɓangare ne na tallafawa tattalin arzikin cikin gida da ƙarfafa masana’antu.
- Jami’ar Danfodiyo Ta Musanta Harin ‘Yan Bindiga A Harabar Jami’ar
- Matatar Dangote Ta Fara Fitar Man Fetur Dinta Zuwa Kasashen Afrika
Dangote ya tabbatar da cewa masana’antar za ta ci gaba da samar da kayayyaki masu inganci waɗanda suka dace da muhalli, tare da ƙara samarwa don wuce buƙatun man fetur na cikin gida da tabbatar da wadatarsa.
Masana’antar ta cimma yarjejeniya da ƙungiyar dillalan man fetur ta Nijeriya (IPMAN) kai tsaye daga masana’antar bayan makonni ana tattaunawa.
Sanarwar ta jaddada cewa masana’antar za ta ci gaba da ƙoƙari don tabbatar da samuwar fetur mai inganci da ɗorewa, tare da taimakawa wajen bunƙasa tattalin arziki da rage tsoron ƙarancin man fetur a kasuwa.