Gwamna Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya aza tubalin gina katafaren ginin Majalisar Dokoki da Babbar Kotun Jiha a wani bangare na gina cibiyoyin rukunan gwamnati 3 wanda zai kunshi bangaren zartarwa, da sashin majalisa da kuma na shari’a.
Da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Inuwa ya bayyana kudirin gwamnatinsa na samar da kyakkyawan yanayin aiki ga dukkan bangarorin gwamnati, don ba su damar gudanar da aiki yadda ya kamata.
- Dikko Radda Ya Bai Wa Gwarazan Hikayata Kyautar Kudi
- Ruguza Tsohon Tsari Na Duniya Zai Haifar Da Ci Gaban Afirka
Gwamnan ya bayyana cewa an ba da kwangilar gina babbar kotun jihar ne kan kudi naira biliyan 14 da miliyan 900, yayin da ginin majalisar zai lakume naira biliyan 14. da miliyan 5.
Ya yi amfani da wannar dama wajen bayyana aniyarsa ta maida tsohuwar Majalisar Dokoki da Babbar Kotun jihar zuwa asibiti da kwalejin ‘yan mata, don amfanin al’ummar yankin da kewaye.
Da yake bayyana aikin a matsayin wani matakin da ba a taba ganin irinsa ba na cike gibin ababen more rayuwa, Inuwa ya ce, “Tun da aka kirkiro ta shekaru 28 da suka gabata, Jihar Gombe ba ta taba ganin irin wannan aiki ba don samar da yanayin aiki da ya dace ga shugabanni da ma’aikatan gwamnati a jihar.
“Ta hanyar samar musu da wuraren aiki na zamani kamar ko’ina a duniya, muna kara tabbatar da aniya da jajircewarmu na karfafa tsarin gudanar da mulki da ke tabbatar da dimokuradiyya da ci gaban al’umma.
“Tare da wadannan ayyuka, muna fatan bude wani sabon babi da zai kara karfafa alaka da bai wa kowane rukunin gwamnati damar gudanar da ayyukansa yadda ya kamata.
“Wadannan ayyuka ba kawai gine-gine ne na zahiri ba, ginshiki ne na samun ci gaba mai dorewa, inda jagoranci da dimokuradiyya za su karfafa, kuma kowane dan kasa ya samu damar ci gaba yadda ya kamata,” in ji shi.
Gwamnan ya yaba da kyakkyawar alakar aiki da ke tsakanin bangaren zartaswa da sauran bangarorin gwamnati, wanda ya ce ya taimaka wajen cimma nasarorin da gwamnatin mai ci take samu.
Shi ma kwararren mai sanya ido kan aikin daga kamfanin Artec Practice Limited, Arc. Oni Oluseyi, ya ce aikin babbar kotun jihar gini ne na zamani wadda ya kunshi dakunan shari’a 12 masu iya daukar mutane 60, da dakin taro, da ofisoshin alkalai da sauran manyan jami’an shari’a, da dakin karatu na zamani (E-library) da kuma dakin ganawa da manema labarai da dai sauran wurare.
Dangane da ginin majalisar dokokin jihar kuwa, kwararren ya ce an tsara ginin ne zuwa bangarori biyu da suka kunshi zauren majalisa, da ofisoshin kakakin majalisa, da na mataimakinsa da sauran mambobin majalisar, da dakin karatu, da na taro, da wuraren liyafa da dakunan taro, da asibiti da zauren ganawa da manema labarai da dai sauransu.
Manajojin Daraktocin kamfanonin gine-ginen da aka bai wa kwangilolin, Kamfanin Datum Construction, Daher Kaworma da takwaransa na Kamfanin GMC George Maroum, sun tabbatarwa gwamna da al’ummar jihar cewa za su gudanar da ayyuka masu inganci da nagarta.