Wasu jiga-jigan kungiyar tuntuba ta Arewa (ACF) sun yi wani sabon yunkuri na mara baya ga dan takarar shugaban kasa daga arewa a zaben 2027, wanda suke ganin cewa dan yankin arewa ne kadai zai iya kishin magance tarin matsaloli da yankin ke fuskanta a halin yanzu.
Wannan matsayi ya fito ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun, Sakataren Yada Labarai na ACF na kasa, Farfesa Tukur Muhammad Baba, kuma ya raba wa manema labarai bayan taron majalisar zartaswa ta kasa da kungiyar ta gudanar a Kaduna.
Sanarwar ta ce, taron majalisar zartarwa ta ACF, ya yi bitar abubuwan da ke faruwa a arewa da ma kasa baki daya.
“An gudanar da taron majalisar zartarwa ta kasa na kungiyar ACF a hedikwatarta da ke Kaduna a ranar Laraba 20 ga Satumba, 2024. Wakilai a taron sun fito ne daga jihohin arewa da kuma mambobin kungiyar da ke zaune a kasashen waje, wanda shugaban majalisar zartarwa ta kungiyar, Mamman Mike Osuman, ya jagoranta. Taron ya duba ayyukan ACF tun daga taron na Mayun 2024.”
“A jawabinsa na bude taron, shugaban ya yi maraba da mambobin kungiyar tare da nuna gamsuwa da sake farfado da harkokin kungiyar ACF a matsayinta na babbar kungiyar da ke kare muradu, al’adu da zamantakewar al’umma, wadda ke kokarin hada kan al’ummar arewa daban-daban da mabanbantan ra’ayi da manufa daya, tare da hadin kai wajen ganin an cimma nasarar gudanar muradun al’ummar arewa a cikin Nijeriya. Shugaban ya ja kunnen ‘yan kungiyar da su ci gaba da mai da hankali, musamman kan muradun arewa da kuma manufofin ACF, domin akwai abubuwa da yawa da ya kamata a yi kuma lokaci ya kure.
“Shugaban ya umurci sauran shugabannin kungiyar na rassa daban-daban su kasance cikin manufa guda, tare da kawar da bambance-bambancen addini da na kabilanci, amma su yi kokarin tabbatar da dangantaka mai kyau da gwamnonin jihohi.
“Daga wurin taron, an tattauna batun yanayin yadda al’ummar arewa da ma Nijeriya suke fuskar, inda aka mayar da hankali kan tattalin arziki, yanayin da ake ciki, tsaro, kalubalen zamantakewa, zaman lafiya, da ci gaban siyasa.
“Taron ya yi nuni da cewa, al’ummar arewa na ci gaba da fuskantar tabarbarewar al’amura, kasancewar a halin yanzu yankin ya fi samun koma-bayan tattalin arziki idan aka kwatanta da sauran sassan Nijeriya.
“Yankin na fama da matsananciyar rashin wadataccen abinci, kuma matasansa ba su da ilimi da sanin makamar aiki. Yanzu ne lokacin yin tunani. Duk da irin halin da Arewa ke ciki na fuskantar kalubalen tattalin arziki, manufofin gwamnatin tarayya na ci gaba da dagula al’amura, tare da nuna rashin sanin ya kamata dangane da halin da al’ummar arewa ke ciki.
“Kira ga gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ta sake duba al’amura da sake tsara alkiblar manufofinta na tattalin arziki ta yadda za su dace da bukatun al’ummar arewa.
“Muna kira da babbar murya ga gwamnonin jihohin arewa da su rungumi tsarin aiwatar da manufofi masu karfi, tare da hadin kai, musamman ta fuskar tsaro, ilimi, koyon sana’o’i, noma, da harkokin kiwon lafiya.
“Rashin wadatar wutar lantarki zai ci gaba da kawo cikas ga kokarin da ake na magance fatara, rashin aikin yi, da rashin ci gaba a yankin. Wadannan dole ne a magance su cikin gaggawa.”
Kungiyar ta ce wannan mataki na da nufin ceto yankin arewa daga gazawar shugabanci da matsalolin da ake fuskanta.
ACF ta nuna goyon bayanta ga kungiyar ‘League of Northern Democrats’ (LND), wata sabuwar kungiya da ta dukufa wajen magance matsalolin yankin arewa, ciki har da rashin aikin yi, ilimi, da tasirin siyasa.
Kawunan dattawan arewa dai ya rabu a zaben 2023, duk da dai ACF da NEF sun bayyana cewa bakin su a hade yake, amma kowa ya nuna cewa ba haka ba ne.
Ta ina kangiyar ACF za ta fara? Sabon abu ne za ta zo da shi ko kuma ta yaya lamarin zai tabbata?
Tun da na farko, akwai kalubalen hadin kai a arewa, saboda yanayin yadda aka farraka kabilu, maimakon kishin arewa, wanda a baya babu maganar kai dan arewa ta kudu ne ko ta tsaki. Amma yanzu da yawan kabilu a arewa idan a ce musu su ‘yan arewa, sai su ce su ba ‘yan arewa ba ne.
Wannan yunkuri abu ne mai kyau kamar yadda wasu yankuna suke yi. Kungiyar Yarbawa an ga yadda take magana da murya daya. Haka nan kungiyar dattawan Ibo suma suna da wannan. Amma yanzu a arewa babu kungiya guda daya tilo, wanda ko a kungiyar dattawan arewa sun rabu kashi buyu, haka kuma kungiyar Fulani ta Meyatt Allah ta rabu kashi-kashi.
Masana suna ganin cewa tana ita za a fara irin wannan yunkurin a yankin arewa.