Sanata Bala Mohammed, Gwamnan Jihar Bauchi, ya samu lambar yabo ta Leadership ta Gwamnan Shekara ta 2024.
Gwamna Bala ya samu wannan lambar yabo saboda irin sauye-sauyen da ya kawo a ɓangarori daban-daban, ciki har da ababen more rayuwa da ilimi da lafiya da kuma tsaro. Wannan shi ne karo na biyu da aka karrama shi da wannan lambar yabo saboda jagorancinsa mai cike da hangen nesa da sadaukar da kai wajen bunƙasa rayuwar jama’a.
- Ɗangote Ne Gwarzon Jaridar LEADERSHIP Na Shekara Ta 2024
- Gwarzon Ma’aikacin Gwamnati 2024: Shugaban Kwastam, Alh. Bashir Adewale Adeniyi
Tarihi da Siyasa A Taƙaice
An haifi Bala Mohammed a Duguri, Alkaleri Jihar Bauchi, a ranar 5 ga Oktoba, 1958. Ya yi karatu a shashen harsuna na Jami’ar Maiduguri, sannan ya fara aikinsa a matsayin ɗan jarida, inda ya yi aiki a kamfanin dillancin labarai na ƙasa (News Agency of Nigeria), da wasu kafafen irinsu The Mirage da Democrat. A matsayinsa na ɗan jarida, ya gina fahimta sosai kan matsalolin da suka shafi jama’a, wanda ya ja hankalinsa zuwa shiga siyasa.
Bala, Ya fara siyasarsa a 2007, tsohon ɗan siyasa, ya zama Sanatan Bauchi ta Kudu, inda ya yi fice wajen gabatar da ƙudirori kan ayyukan gwamnati da yaƙi da cin hanci da rashawa. A 2010, ya zama Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), inda ya kawo sauye-sauye a harkokin sufuri da gidaje da kula da muhalli. Daga cikin muhimman nasarorin da ya samu akwai ƙaddamar da hanyar sufurin jirgin ƙasa (Abuja Rail Mass Transit System), wanda ya rage cunkoso a birnin Abuja.
A 2019, Bala Mohammed ya zama gwamnan Jihar Bauchi, inda ya mayar da hankali kan inganta rayuwar jama’a ta hanyar ayyukan ci gaba a fannonin ilimi da lafiya da noma da bunƙasa fannin tsaro.
Ilimi da Lafiya
Gwamnatin Kauran Bauchi ta gina tareq da gyara ajujuwa sama da 5,000, sannan ya rage yawan yara da ba sa zuwa makaranta daga miliyan 1.2 zuwa 521,000. A ɓangaren lafiya kuwa ya gyara tare da gina sababbin asibitoci da cibiyoyin lafiya sama da 1,000, inda ya hakan samar da sauƙi ga al’ummar karkara wajen samun kulawa a fannin lafiya.
Ababen More Rayuwa da Noma
A ƙarƙashin mulkinsa, Ƙauran Bauchi ya gina sababbin hanyoyi da gadoji da hanyoyin karkara, ciki har da gadojin sama guda biyu a tsakiyar birnin jihar Bauchi, don rage cunkoson ababen hawa. Ya tallafa wa manoma ta hanyar rage farashin taki da kayan aikin gona da ba su horo kan fasahohin zamani, wanda hakan ya ƙara samar da yawan abinci da ayyukan yi a jihar.
Tallafi ga Mata da Matasa
A ƙarƙashin shirin Kaura Economic Empowerment Programme (KEEP), an samar da jari da bayar da horo ga matasa da mata don su kafa ƙananan sana’o’i. Kazalika, ya bayar da tallafin Keke NAPEP sama da 1,000 ga matasa ba tare da sanya ƙarin kuɗaɗe ba, don su samu damar dogaro da kansu.
Sanata Bala Mohammed, gwamna ne mai ƙwazo da himma wajen ziyartar wuraren aiki da sauraron ƙorafe-ƙorafen jama’a. Wannan salon jagoranci ya kawo amincewa daga jama’ar da ya ke mulka, inda suke ganinsa a matsayin jagora da ke kula da buƙatunsu.
A yau, Jihar Bauchi ta zama ɗaya daga cikin jihohin da suka fi zaman lafiya a Nijeriya. Gwamna Bala Mohammed ya gina rayuwar jama’a ta hanyar bijiro da ayyukan ci gaba da kawo ci gaba mai ɗorewa, ya mayar da Jihar Bauchi jiha abar koyi a Arewacin Nijeriya. Wannan nasarar ta fito fili daga irin hangen nesansa na shugabanci, tare da aiki tuƙuru da bayar da kulawarsa ga buƙatun jama’a.