Saboda zuba jari mai yawa a fannin haƙar ma’adanai da man fetur a faɗin Afirka, ya sa ake masa laƙabi da “Jagoran Haƙar Ma’adanai da Man Fetur na Afirka,” da kuma rashin tsoro wajen zuba dukiyarsa a harkar kasuwanci.
Benedict Peters, wanda ya kafa ya ke kuma jagorantar Aiteo/Bravura, ya samun lambar yabo ta Gwarzon Ɗan Kasuwa na Shekarar 2024 ta Jaridar Leadership.
- Gwamnan Shekarar 2024: Sanata Ademola Jackson Nurudeen Adeleke
- Ɗangote Ne Gwarzon Jaridar LEADERSHIP Na Shekara Ta 2024
Benedict Peters yana daga cikin shahararrun mutane a harkar kasuwanci a Nijeriya. Kasuwanci cike da ƙwarewa da masaniyar tafiyar da harkokin kasuwanci, Peters na daga cikin sunayen da suka shahara sosai a Nijeriya da ma Afirka baki ɗaya. Ya zama sananne a matsayin babban ɗan kasuwa wanda ke da hannun jari a fannonin man fetur da haƙar ma’adanai a Nijeriya da Ghana da Zimbabwe da Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kongo da Zambiya da Tanzania da Mozambique da Cote d’Ivoire da Sierra Leone da Guinea Bissau da Namibia da Libya da Afrika Ta Kudu da kuma Switzerland.
Duk da kasancewarsa mai mai ɓoye sirri, Peters na daga cikin manyan ‘yan kasuwa na farko-farko a harkar man fetur da gas. Ya fara aiki a wannan fanni a farkon shekarun 1990, inda ya shiga kamfanin Ocean and Oil Limited (Oando a yanzu) sannan daga bisani ya zama Daraktan Gudanarwa a kamfanin MRS Oil Nigeria Plc.
A matsayinsa na matashin ɗan kasuwa, Peters ya kafa Sigmund Cummunecci a shekarar 1999, wanda daga baya ya zama Aiteo, kamfanin da ke samar da man fetur da gas da aka tace, wanda daga baya ya zama babban mai zaman kansa a fannin man fetur a Afirka.
Peters ya shiga harkar kasuwancin man fetur a shekarar 1999, inda ya fara kasuwancin rarraba man fetur. Duk da haka, Aiteo ya zama kamfanin da ke samar da man fetur mafi girma a Nijeriya a cikin ƙanƙanin lokaci.
A shekarar 2015, Peters ya sayi babban filin mai na OML 29 mai darajar dala biliyan uku. A cikin shekara guda, Aiteo ya ƙara yawan man fetur da ya ke fitarwa daga ganga 17,000 zuwa kusan ganga 70,000.
A matsayin babban mai samar da man fetur, Aiteo ya kai matakin samar da man fetur har zuwa ganga 100,000, wanda ya ninka darajar dukiyarsa zuwa dala biliyan shida cikin shekaru uku. Kamfanin yana shirin zuba dala biliyan 4.3 don sayen sabbin kadarorin ruwa, tare da hasashen samar da kimanin 250,000 bbl/d a nan gaba.
Aiteo Group yana da jari a ɓangarori daban-daban kamar haƙar ma’adanai da noma da gine-gine da wutar lantarki tare da mayar da hankali kan biyan buƙatun al’umma a faɗin Afirka ta hanyar amfani da dabaru da fasaha da ƙirƙire-ƙirƙire da sauransu
Kamfanin yana faɗaɗa zuwa ƙasashe daban-daban a Afirka da ma wajenta. Yana da tasiri a ƙasashen DRC, Ghana da Guinea da Laberiys da Zambiya da kuma Zimbabwe.
Aiteo, ya zama babban kamfani da ke aiki a fannin samar da man fetur da gas, yana da cikakken tsarin aiki daga samar da wutar lantarki da rarraba kayayyakin man fetur.
Kamfanin yana aikin adana kayayyakin man fetur da samar da wutar lantarki da rarraba ta, ajiye LPG a manyan wurare da kasuwancin kayayyakin man fetur da rarraba su.
Aiteo Group yana da kamfani na samar da wutar lantarki – Aiteo Power Generation Company Ltd, wanda ya samu nasarar cin gasar Alaoji Power Generation Company. Wannan ya bayar da damar haɗa ayyukan kamfanin wajen gina cibiyar samar da wutar lantarki a yankin Neja Delta. Sannan yana amfani da wutar lantarki da albarkatun gas daga wuraren haƙar mai.
Peters yana shirin bunƙasa amfani da gas da man fetur da kwal ta hanyar samar da wutar lantarki da rarraba ta a Nijeriya da sauran ƙasashen Afirka ta Yamma. Wannan shirin yana nufin samar wa mutane miliyan 7.6. tsayayyiyar wutar lantarki. Shirin samar da wutar lantarki zai mayar da hankali a Afirka kuma yana fatan samar da wutar lantarki a duk faɗin nahiyar.
Manufar Peters ita ce ganin cewa manyan rukunin gas na Afirka an bunƙasa su gaba ɗaya, ta yadda wutar lantarki za ta samu a ko’ina a faɗin nahiyar.
Kamfaninsa yana ƙoƙarin haɓaka dukkanin ayyukansa ta hanyar haɗin guiwa da manyan kamfanoni na duniya domin warware matsalolin gas.
Wannan yana nufin zuba jari mai yawa a wuraren tattara gas da sarrafawa, samar da LPG, adana shi da rarrabawa. Kazalika yana gina bututun mai da sarrafa NGL da kuma sufuri.
Peters ya samu wata babbar nasara ta hanyar haɗin guiwa da NNPC wajen ƙaddamar da sabon nau’in mai, mai suna Nemb; ta wannan haɗin guiwa ne kamfanin ya ƙara yawan man fetur ɗin da yake samarwa.
Aiteo, wanda shi ne kamfani mafi girma wanda yake samar da man fetur a Afirka, yana taka muhimmiyar rawa a masana’antar mai ta nahiyar, inda yake samar da kusan ganga 100,000 a kowace rana da bayar da gudummawa fiye da kashi 5 cikin 100 na samar da man fetur na Nijeriya.
Peters ya samu wani babban fili wanda zai ke amfani da shi wajen samar da gas a Mazenga a ƙasar Mozambique, wanda shi ne mafi girma a ƙasar. Sayen ya kammala ne bayan yarjejeniya da kamfanin man fetur na ƙasar, Empresa Nacional de Hydrocarbon (ENH), wanda ya sa kamfanin Aiteo ya zama mai gudanar da aikin.
Peters ya faɗaɗa kasuwancinsa zuwa fannin haƙar ma’adanai ta hanyar Bravura Holdings. Ya zuba jari mai yawa a fannin uranium da platinum da lithium da azurfa da ƙarfe da kuma zinariya a faɗin Afirka.
Peters ya samu kyaututtuka masu tarin yawa, ciki har da lambar karramawa ta ‘Jagoran Man Fetur da Gas na Afirka’ daga Forbes a 2018. Sannan ya kasance ɗaya daga cikin fitattun mutane 50 masu tasiri a duniya.