Odumodublvck, haifaffen Tochukwu Gbobemi Ojogwu ne, an haife shi ranar 19 ga watan Oktoban 1993, fitaccen mawaƙi ne a masana’antar waƙa ta Nijeriya.
Shahararsa ta sake bayyana darajar masana’antar waka ta zamani a Afirka a bangaren hip-hop da highlife da drill da kuma Afrobeats.
- Gwarzon Kamfani A Shekarar 2024: AVSATEL Communications Limited
- Gwarzon Wasannin Motsa Jiki Na Shekarar 2024: Bambo Akani
Wannan basira da hazaka da Odumodublvck, ta sanya masoya sauraron waƙoƙi a ƙasa da ƙetare nishaɗi, hakan ya tabbatar da shi a matsayin ɗaya daga cikin ƙwararrun masu fasaha na wannan ƙarni.
Raira wakoki na ƙashin kai, ita ce babbar nasarar Odumodublvck. Yana zurfafa tunani wajen zaɓen kalmominsa da suke ɗauke da ma’anoni masu motsa zuciya da nuna juriya da rajumta da kuma bayyana al’adu da ke ƙara ɗaukaka daraja da gogewar mutanen yankin nahiyar Afirka.
Kazalika, yana jan hankalin masu sauraro da kalamai masu ciki da fasaha. Wannan hikimar da ba a taba ganin irinta ba, ta bayyana irin ɗimbin hikima da basirarsa wacce ta keɓe shi a irin wannan masana’anta mai mahimmanci.
Yadda Odumodublvck ke raira waƙe tare da hawa kiɗa ya bayyana hazaƙarsa da ƙwarewarsa a waƙa. A cikin 2022, ya samu
gagarumin ci gaba ta hanyar sanya hannu tare da ‘Native Records’, – Lambar yabo ce da aka keɓe ta ga ‘yan Nijeriya masu hazaƙa don ɗaukaka hazaƙarsu a nahiyar Afirka baki ɗaya.
Bugu da kari, haɗin kansa da ‘Def Jam Recordings’ – wacce kasaitacciyar cibiya ce ta duniya a masana’antar waƙa, ta kara tabbatar da shahararsa a masana’antar a lokacin da ya tattaɓa hannu kan yarjejeniya ta musamman da cibiyar a 2023.