Nakasa na nufin tawaya ko gaza ko raunana, (CNHN, 2006: 356). Saboda haka, nazarin nakasa fage ne da ke ƙoƙarin bayyana batutuwan da suke ɗamfare da zamantakewa da al’adu da siyasa waɗanda suka jiɓanci yadda ake kallon nakasa da nakasassu.
Ita kuwa karin magana ɗaya ne daga cikin sassan adabin baka da Hausawa ke amfani da ita domin ƙawata zance ya yi armashi.
- Sabon Albashi: NLC Ta Fara Yajin Aiki A Jihohi 15 Na Nijeriya
- Majalisar Dokokin Kano Ta Yi Watsi Da Ƙudirin Gyaran Dokar Haraji A Nijeriya
Ke nan, karin magana zance ne a dunƙule mai faffaɗar ma’ana, ƙunshe da sharhi kan rayuwar al`umma cikin hikima da fasaha. Shi ya sa karin magana ya zama rumbun ajiye al`adu da tunani da ɗabi’u da kuma tarihin al`umma.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta ware ranar 3 ga watan Disamba ta kowace shekara a matsayin Ranar Nakasassu ta Duniya. Hakan kuwa ya samo asali ne tun daga shekarar 1992, inda aka ware ranar da manufar fahimtar batutuwan da suka shafi nakasa da kuma tallafa wa matsayi da haƙƙoƙin nakasassu.
Wata manufar ware ranar kuwa ita ce, sake wayar da kan al’umma game da irin alfanun damawa da nakasassu cikin duk sha’anonin zamantakewa da siyasa da tattalin arziƙi da duk al’amuran rayuwar yau da kullum.
Irin wannan rana a kowace shekara, tana da taken da ake mayar da hankali a kai. Shi ya sa a wannan shekara ta 2024, taken ranar shi ne; Tabbatar da damar shugabanci ga nakasassu domin ɗorewar al’ummar da take tafiya bai-ɗaya a gobe. Saboda haka, ‘yar tsarabar tamu ta yau, wato Ranar Nakasassu ta Duniya, wadda ta ƙunshi fitila da ta haska ma’anar nakasa da nau’o’inta a al’adance, da kuma yadda ake kallon nakasar a karin maganar Hausa.
Nakasa Bisa Faifai
Nakasa kalmar Larabci ce da Hausawa suka aro suke amfani da ita. A Larabce, kalmar tana nufin rangwamen wani abu, wato rashin cikar wani abu. Wannan kalmar Hausawa sun aro lafazi da ma’anarta suke amfani da ita kamar yadda take a Larabci.
Sai Bahaushe ya dubi kalmar ta fuskar kalmomin fannu waɗanda suka danganci jikin ɗan Adam, da ma’anar rangwamen ɗaya daga cikin gaɓuɓuwan jikin mutum kamar ido ko yatsu ko hannu ko ƙafa ko hankali a sanadiyyar wata cuta ko haɗari ko shaye-shaye (Sarkin Gulbi, 2007:37). A ma’ana ta zahiri kuwa, nakasa na nufin tawaya ko gaza ko raunana (CNHN, 2006: 356).
Saboda haka, nakasa ita ce wata tawaya a cikin ayyukan jiki ko kuma wahalhalun da ake samu wajen wani sanannen aikin da mutum kan samu wajen gudanar da hidima ko aiki. Shi ya sa Bunguɗu (2015) ya ce, duk wata tawaya da aka samu a wata gaɓa ta jikin mutum ana kiran ta nakasa, wannan kuwa har da taɓin hankali.
Kakkaɓe Ɓurɓushin Nakasa a Karin Magana
Da yake adabin Bahaushe bai bar komai ba dangane da rayuwarsa ta yau da kullum. An lura cewa mutanen da suka sami kansu cikin wata halayyar rashin lafiya na nakasa, rayuwarsu ta bambanta da ɗabi’un rayuwar sauran masu cikakkiyar lafiya(Bunza, 2006: 191).
Wannan shi yake gina irin tunanin da ake ɗora karin maganar Hausa mai ɓurɓushin nakasa bisa kai, shi ya sa akan sami karin magana da Bahaushe ke ambaton wasu masu nakasa ga jiki don a tausaya masu, ko domin a nuna halinsu, ko wautarsu, ko alaƙarsu (Koko, 2011: 24). A nan, za a taƙaita ga ɓurbushin makanta da kuturta da gurgunta da kurumta ne a karin maganar Hausa.
Makanta Nakasar Ido
Makanta na nufin rashin gani (CNHN, 2006:322). Saboda haka makaho shi ne wanda ba ya gani, mace ana ce da ita makauniya, jam’i makafi (CNHN, 2006: 321). Makanta nakasa ce da ta shafi rasa idanuwa biyu saboda kamuwa da ciwon ido ko haɗari a lokacin yaranta ko bayan girma (Sarkin Gulbi, 2007: 37).
A cewar Bunza (2006:192), makanta ba wata nakasa da ke taɓa hankali ba ce, ko ta raunana tunanin masu ita. Makaho a kallon Bahaushe mutum ne mai yawan musu, da wayo da son jayayya.
Watakila saboda rashin ganin da ba ya yi, yana ganin kamar ana fakewa gare shi ana raina masa wayo. Don haka, duk wani abu masu idanu suka faɗa sai ya yi musu don a san ba a fi shi ba (Bunza, 2006:192).
Saboda haka, wasu karin maganar masu ɓurɓushin makanta suna ƙunshe ne da hoton irin wannan wayo da musu da son jayayya na makafi ko makaho kamar yadda aka san su a zahirance. Misali:
Ɗinyar makaho ta nuna a hannunsa.
Hannu da hannu cinikin makaho.
In ka ji makaho ya ce a yi wasan jifa, to ya taka dutse.
Makaho na da ido amma ba na ganin gari ba.
Sau ɗaya gyaɗar makaho ke ƙonewa.
Da zarar ka ji batun ‘ɗinyar makaho ta nuna a hannunsa’, to akwai batun tsananin wayo da rashin yarda. Domin makaho ba ido ne da shi ba, don haka ɗinyarsa ta nuna a hannunsa kawai. Haka batun yake in an ce ‘hannu da hannu cinikin makaho’. Haka nan, wayon makaho ya sa shi takalar wasan jifa idan ya taka dutse, wayon nasa kuma shi ya sa bai yarda gyaɗarsa ta ƙone sau biyu ba.
Abin lura a nan shi ne, ire-iren waɗannan karin magana suna jaddada cewa nakasa ba kasawa ba ce, don kuwa ko da makaho ya rasa ido, sai aka same shi da wayo wanda wani mai idon ma bai da shi. Ga shi kuma da tsayin daka, shi ya sa ma yake da musu da son jayayya.
Har ila yau, akwai kuma wasu karin maganar da ke bayyana hoton rashin gani ga makaho da kuma yadda rashin ganin ya zame masa ƙalubale. Misali:
Allah na gani ake cutar makaho.
Allah shi ke gyara tuwon makauniya ya yi daɗi.
Babu ruwan makaho da madubi ko an sawo daga Turabulus.
Bakin rijiya ba wurin wasan makaho ba ne.
Na raina damben makaho ko ya shirya.
Rashin sani, makaho ya taka sarki.
Waɗannan misalan karin magana sun nuna cewa duk da irin wayo da musu na makaho amma haka nan ake cutarsa saboda ba shi da idon da zai gani a lokacin da ake shirin cutarsa ko ake cutar da shi. Shi ya sa ma dogaro ga Allah shi ke sanya har makauniya ta tuƙa tuwo ya yi daɗi, ba don tana gani ba, kamar yadda makaho ba shi da idon da zai iya duba fuskarsa a madubi ko daga ina aka ƙera madubin kuwa.
Hakan ya sa bakin rijiya bai zama wurin wasan makahon ba, gudun kada ya faɗa. Kazalika, in ba a rashin sani ba, me zai kai makaho taka sarki?
Abin lura a nan shi ne, ire-iren waɗannan karin magana ana amfani da su a zantukan yau da kullum domin yi wa al’umma hannunka-mai-sanda domin su tsinkayi wasu darussa na rayuwa, amma a ma’ana ta zahiri, maganganun suna fito da ɓurɓushin nakasa cikinsu ta hanyar bayyana rangwamen gani da abin da ya haifar ga makafi. Duk da dai Allah da ya yi makaho shi ke masa ɗan jagora.
Kuturta Nakasar Yatsu
Kuturta wata irin cuta ce da ake ɗauka daga iska wadda take ɓata fuska da sauran jiki, tana riƙe jijiya ta guntule yatsu. Saboda haka kuturu shi ne mutumin da cutar kuturta ta kama shi har yatsunsa suka gutsure, mace kuma ana ce da ita kuturwa, jam’insu kuma kutare (CNHN, 2006:258).
Kuturu a al’adar Bahaushe mutum ne mai saurin suƙewa, da fushi da baƙar magana. A ganin Bahaushe, wannan ba ta rasa alaƙa da yanayin cutar da ke damun sa ba. A mizanin zuciyar kuturu ta wuce min sharrin domin ko da kansa yana fushi balle da wani can da ba shi ba.
Duk wata magana, ko aiki, na kutare Bahaushe na ɗora shi a kan sanin da ya yi wa kuturu na saurin fushi da zuciya (Bunza, 2006:192). Saboda haka, karin magana mai ɓurɓushin kuturta ana gina su ne bisa wannan tunani na sanin da aka yi wa kuturu na saurin fushi da zuciya da kuma baƙar magana. Misali:
An ce da kuturu ga yatsu, ya ce ; “Me zan yi da su?”
“Da haka muka fara”; kuturu ya ga mai ƙyasfi.
Kowa ya ci ladar kuturu ya masa aski.
Naci, damben kuturu.
“Yaushe kuma?”; an ce da kuturu ka gama lafiya.
In ba a kwaɗo da kuturu, a ba shi daddawarsa.
Waɗannan misalai sun nuna ƙarara yadda kuturu ke da saurin fushi a zahiri, shi ya sa ma a ganinsa ba abin da zai yi da yatsu, tun da bai da su. Ƙyasfi wata cuta ce da take haifar da tamuƙewar fata da sauya mata launi wanda ya bambanta da nata na asali.
Da yake ita ma cutar kuturta tana da alaƙa da tamuƙewar fata kafin daddatsewar gaɓoɓi, Shi ya sa da ‘kuturu ya ga mai ƙyasfi, ya ce su ma kutaren da haka suka fara’. Bugu da ƙari, lura da naci da fushin kuturu ya sa aka ƙirƙiri ‘naci damben kuturu’, haka nan ko da ‘aka ce wa kuturu ka gama lafiya; baƙar magana ya mayar cewa; ‘yaushe kuma?’.
Shi a ganinsa, tun da ya kuturce, batun gamawa lafiya bai ma taso ba! Saboda haka, sanin hali ne ya sa karin maganar Hausa ya nuna in har ‘ba a kwaɗo da kuturu, to a ba shi daddawarsa’ shi ne mafi a’ala.
Wani abin lura kuma shi ne wasu karin maganar ana gina su ne ta dubi da irin larurar da kuturun ke ɗauke da ita ta rashin yatsu, sai karin maganar ya bayyana gazawarsa kan wani al’amari. Misali:
Allah da ikonsa kuturu ya hau giwa.
Ba zai yiwu ba, wankan kuturu da sabulu.
Komi da mazauninsa, an sa wa kuturu ankwa ta saɓule.
Ƙwace goruba hannun kuturu ba wani abu ba ne.
Yau da kallo, an sa kuturu murzar barkono.
Kuturu ya so dambe babu yatsu.
Ba a yabon ɗan kuturu, sai ya girma da yatsu.
Waɗannan misalai duk sun nuna a zahirance yadda kuturta a matsayin nakasa ta zama ƙalubale ga rayuwar masu fama da ita (kutare), ta yadda nakasar take hana su gudanar da wasu al’amuran da masu yatsu ke gudanarwa.
Alal misali, in dai ba ikon Allah ba, ta yaya kuturu zai hau giwa tun da ba yatsu ne gare shi ba? Haka kuma, sabulu yana da santsi shi ya sa ba zai yiwu kuturu ya yi wanka da shi ba don ba shi da yatsun da zai riƙe sabulun. Duk dai cikin rashin yatsun; idan aka sa wa kuturu ankwa saɓulewa za ta yi, cikin sauƙi za a ƙwace masa goruba, ba kuwa zai iya murzar barkono ba; kamar yadda ko ya so dambe ba ya iyawa tun da duk ayyuka ne da ake gudanar da su da taimakon yatsu.
Da yake ma ita cutar kuturta ana gadonta, shi ya sa ‘ba a yabon ɗan kuturu, sai ya girma da yatsu’. A dunƙule, waɗannan misalai na karin magana, sun bayyana yadda kuturta (nakasa) ta zama barazana ko ƙalubale ko kuma tasku ga masu nakasar kuturta wajen gudanar da wasu al’amura na rayuwa.
Gurgunta Nakasar Ƙafa
Gurgunta nakasa ce wadda kan hana wa mutum tafiya daidai, wannan daidai yake da gurguntaka ko gurgunci ko ɗingishi. Kenan gurgu shi ne wanda yake tafiya ba kamar yadda jama’a ke yi ba, saboda illar da ta sami ƙafa ko ƙafafunsa. Idan mace ce kuma ana ce da ita gurguwa, jam’i guragu (CNHN, 2006:176). A al’adance kuwa, gurgu shi ne wanda ya rasa ƙafafunsa biyu, ko ya rasa ɗaya ita kawai.
Ta karye ne, ko ta shanye, ko tsawonta bai kai ba, duk gurgu ne a al’ada. Al’adar Bahaushe na kallon gurgu wani irin shaƙiyyi na musamman, kuma ɗan fitina da jidali. Duk wata faɗa aka ce wa Bahaushe da gurgu ciki, ba ya musu balle ya yi jayayya don kare gurgu (Bunza, 2006:192).
Irin wannan tunani ya haifar da karin magana kamar, ‘Maƙetaci mijin gurguwa, wanda ya sayar da jaki ranar tafiya.’
Bugu da ƙari, duk wani lamari na tafiya ko amfani da ƙafa ba ya zuwa da sauƙi ga gurgu, shi ya sa galibi karin magana mai ɓurɓushin gurgunta take bayyanawa ƙarara yadda lamarin yake ga gurgu. Misali;
Da kamar wuya, gurguwa da auren nesa.
Gurgu ba ya koya wa gurgu tafiya.
Gurguwar tsanya da wuri take fara ɓula/tiƙa.
Gurgu bai canza tafiya.
Kaɗan kenan, an wa gurgu ƙafar laka.
A waɗannan misalai an nuna a fili yadda auren nesa ya zamar wa gurguwa jidali musamman a zamanin da, zamanin da ake tafiyar ƙasa. Idan kuwa har gurgu bai iya tafiya ba ko kuma yana tafiyar ba kamar yadda lafiyayye ke yi ba, to ta yaya zai koya wa wani gurgun tafiya? Kai hatta tsanya, in dai gurguwa ce, to da wuri take fara tiƙa.
Kuma duk yadda ya so, gurgu ba ya canza tafiya, wannan ya jaddada yadda tafiya ko duk wani amfani da ƙafa ke yi yana zama babban ƙalubale ne ga gurgu sakamakon nakasar da yake tare da ita (gurgunta).
Kurumta Nakasar Kunni
Kurumta nakasa ce da take da alaƙa da lalacewar kunne ta yadda zai daina jin motsi ko maganar wani. Saboda haka kurma shi ne mutumin da ba ya jin magana sam, ko sai an yi magana da ƙarfi kafin ya ji, kuma ba ya iya magana sosai yadda za a fahimta (CNHN, 2006:256).
A wasu lokutan, akan kira mutumin da ba ya ji sosai kuma ba a gane maganarsa bebe, mace kuwa bebiya, yayin da jam’insu ke zama bebaye (CNHN, 2006:43). Ke nan, wanda bai ji gaba ɗaya shi ne kurma, mai ji kaɗan-kaɗan kuma shi ne bebe.
Da kurma da bebe duka al’ada gurbin mahaukata ta aje su. Ba mahaukata ne tuburan ba, amma dai ana yi masu uzuri ga ayyukansu idan sun ɗan aro na mahaukata. Idan aka ga mutum kurma ne al’ada na yi masa uzuri, domin rashin ji na taɓa hankali (Bunza, 2006:192).
Irin wannan tunani da kallon da ake yi wa kurame da bebaye, suna fitowa ƙarara a zubin wasu karin magana masu ɓurɓushin nakasa. Misali:
“Gara kowa da ni”, in ji matar bebe.
Muƙami, bebe da rediyo
Ruguduma, an kama kurma da kwartanci.
Duk waɗannan misalai sun nuna irin wannan ‘kallon mahaukata’ da ake yi wa kurame da bebaye. Shi ya sa ma matar bebe take ganin gara kowa da ita, tun da ta san wane ne mijinta. Yayin da ake kallon sabon salo ne ko wani ‘muƙami bebe da rediyo’. Ga kuma wauta ƙarara inda aka kama kurma da kwartanci.
Bugu da ƙari, kuturta kamar sauran nau’o’in nakasa, ana samun karin magana da suka nuna irin tasku da masu fama da ita suke fuskanta yayin gudanar da lamurran rayuwar yau da kullum. Misali:
Abin faɗa na mai baki ne, bebe sai ka dangana.
Allah kaɗai ya san karatun kurma.
Da magana bakin kurma sai ranar da ya sami baki.
Goron magana ga mai baki, kurma sai shi dangana.
Babu shakka waɗannan misalai sun nuna hoton nakasa da kuma gazawar da nakasar ta haifar wa masu fama da ita (wato kutare), a misali na farko mun ga yadda aka nuna in dai abin faɗa ne shi bebe sai dai ya haƙura, kamar yadda shi ma kurma a misali na huɗu aka nuna dangana ce tasa, domin goron magana na mai baki ne.
A misali na biyu kuwa, an nuna cewa Allah ne kaɗai ya san karatun kurma ba mutum ba, tun da mutum ba ya jin sa, don ba furta karatun yake ba. Kenan, sanin abin da ke zuciyarsa sai dai Allah (SWT). Ko da kuwa da magana bakin kurma sai ranar da ya sami baki, kamar yadda aka nuna a misali na uku.
Naɗe Tabarma
Daga abin da ya gabata, an fi mayar da hankali ne wajen kallon tsarin misalan karin maganar da aka kawo, aka fayyace yadda aka sami ɓurɓushin nakasa a zahiri cikinsu. Sa’annan kuma an kalli yadda karin maganar ta fito da ɗabi’u da halayyar masu ɗauke da nau’o’in nakasa kamar yadda al’adar Bahaushe ta bayyana su.
An taƙaita ga nau’o’in nakasa huɗu ne wato gurgunta da makanta da kurumta da kuma kuturta, duk da ba su ke nan ba. Su ma karin maganar da aka buga misalai da su ba su ke nan ba, domin kuwa ba a rasa ruwa a ƙasa sai in ba a tona ba.
Hakan ya sake bayyana yadda ire-iren waɗannan karin magana suke yin tasiri wajen bunƙasa adabin Hausa baya ga nuni ga ɓurɓushin nakasa da suke yi.
Mujaheed Abdullahi Kudan ne ya rubuta wannan muƙalar
+2348069299109, [email protected]