• English
  • Business News
Saturday, June 7, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Dole Ne Amurka Ta Yi Watsi Da Matakin Babakere A Fannin Kimiyya Da Fasaha 

by CGTN Hausa and Sulaiman
6 months ago
in Ra'ayi Riga
0
Dole Ne Amurka Ta Yi Watsi Da Matakin Babakere A Fannin Kimiyya Da Fasaha 
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

A ranar Litinin 2 ga watan nan, gwamnatin Amurka ta sanar da sabon matakin kayyade fitarwa kasar Sin na’urorin latironi, har ma ta kara shigar da kamfanonin Sin kimanin 140 cikin jerin sunaye wadanda ta hana a shigar musu da wadannan kayayyaki daga Amurka. Ban da wannan kuma, ta tsoma baki cikin harkokin cinikayya dake tsakanin Sin da sauran kasashe.

Wannan ne karo na 3 da Amurka ta sanar da irin wannan mataki na kayyade fitarwa kasar Sin na’urorin latironi. Amma Amurka ba ta cimma burinta ba ko kadan.

  • Majalisa Ta Dakatar Da Zama Kan Ƙudirin Dokar Haraji
  • Tinubu Ya Umarci Ma’aikatar Shari’a Da Majalisa Su Yi Aiki Tare Kan Dokar Haraji

Cibiyar nazarin tsare-tsaren duniya ta Amurka ta CSIS ta gabatar da alkaluma dake nuna cewa, daga shekarar 2016 zuwa 2023, yawan kudin cinikin na’urorin latironi tsakanin Sin da kasashe kamar su Amurka, da Japan, da Holland da dai sauransu, ya karu a maimakon raguwa.

Labarai Masu Nasaba

Wannan Kyakkyawan Tunani Ya Shafa Ma Hamadar Sahara Launin Kore

Hadin Gwiwa Hanya Ce Madaidaiciya Wajen Kiyaye Tsaron Shiyya

Ban da wannan kuma, CSIC ta ba da alkaluma masu nuna cewa, tun daga shekarar 2017, yawan kudaden da kamfanoni mafi girma 8 a kasar Sin masu kera na’urorin latironi suka kashe ya karu sosai, inda ya zuwa karshen shekarar 2022, saurin karuwar ya kai kashi 40% bisa na 2021, abin da ya bayyana cewa, Sin na gaggauta kirkiro na’urorin latironi don maye gurbin kayayyaki na Amurka.

Jaridar New York Times ta kasar Amurka ta ba da labarin cewa, sana’ar samar da na’urorin latironi na matukar bukatar hadin gwiwar kasa da kasa, kuma Sin tana mallakar kamfanoni masu samar da kayayyaki mafi yawa a duniya, inda ita kanta wata babbar kasuwa ce. Hakan ya sa, hadin kai da kasar Sin a wannan bangare ba shakka dole ne ake yi shi, kuma ya kasance wani bangare na tsarin samar da kayayyaki a duniya.

Alal hakika dai, duniya na dunkulewa a wannan bangare, amma matakin da Amurka ke dauka ya kawo cikas ga ciniki tsakanin kasa da kasa, kuma ya keta zaman oda da dokar kasuwa, har ma ya haifar da barazana ga tabbacin tsarin samar da kayayyaki a duniya. An yi hasashen cewa, kamfanoni da dama, ciki har da na Amurka a wannan bangare za su yi hasara.

Matsa lamba da Amurka take yi ba zai dakile ci gaban fasaha da kimiyyar kasar Sin ba. Bunkasuwa a wannan bangare na bukatar hadin gwiwar kasa da kasa, ya kamata Amurka ta yi watsi da tunanin babakere, ta kuma rungumi hadin gwiwa, don wannan ita ce hanya mafi dacewa da za ta bi. (Mai zane da rubutu: MINA)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Majalisa Ta Dakatar Da Zama Kan Ƙudirin Dokar Haraji

Next Post

Sin Na Fatan Gwamnatin Amurka Mai Zuwa Za Ta Nuna Kamun Ludayi Mai Kyau A Huldarsu

Related

Wannan Kyakkyawan Tunani Ya Shafa Ma Hamadar Sahara Launin Kore
Ra'ayi Riga

Wannan Kyakkyawan Tunani Ya Shafa Ma Hamadar Sahara Launin Kore

2 days ago
Hadin Gwiwa Hanya Ce Madaidaiciya Wajen Kiyaye Tsaron Shiyya
Ra'ayi Riga

Hadin Gwiwa Hanya Ce Madaidaiciya Wajen Kiyaye Tsaron Shiyya

5 days ago
Akwai Ma’ana Mai Zurfi A Bayan Da’a
Ra'ayi Riga

Akwai Ma’ana Mai Zurfi A Bayan Da’a

2 weeks ago
Ta Yaya Kasashe Masu Tasowa Za Su Iya Tinkarar Yakin Haraji Da Amurka Ta Tayar?
Ra'ayi Riga

Ta Yaya Kasashe Masu Tasowa Za Su Iya Tinkarar Yakin Haraji Da Amurka Ta Tayar?

2 weeks ago
Ingancin Tattalin Arzikin Sin Mai Bude Kofa Na Bayyana Sosai Duba Da Yawan Zuwan Baki Masu Sayayya
Ra'ayi Riga

Ingancin Tattalin Arzikin Sin Mai Bude Kofa Na Bayyana Sosai Duba Da Yawan Zuwan Baki Masu Sayayya

2 weeks ago
Sara Da Sassaka Ba Ya Hana Gamji Toho
Ra'ayi Riga

Sara Da Sassaka Ba Ya Hana Gamji Toho

2 weeks ago
Next Post
Sin Na Fatan Gwamnatin Amurka Mai Zuwa Za Ta Nuna Kamun Ludayi Mai Kyau A Huldarsu

Sin Na Fatan Gwamnatin Amurka Mai Zuwa Za Ta Nuna Kamun Ludayi Mai Kyau A Huldarsu

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Tarayya Da Hadin Gwiwar IFAD Za Su Yi Wa Manoma Rijista Domin Tantance Su

Gwamnatin Tarayya Da Hadin Gwiwar IFAD Za Su Yi Wa Manoma Rijista Domin Tantance Su

June 7, 2025
Dalibai Sama Da Miliyan 13 Ne Za Su Rubuta Jarrabawar Shiga Jami’a Ta Kasar Sin

Dalibai Sama Da Miliyan 13 Ne Za Su Rubuta Jarrabawar Shiga Jami’a Ta Kasar Sin

June 7, 2025
Nazarin CGTN: Jama’ar Duniya Na Ganin Tattaunawa Da Hadin Gwiwa A Matsayin Hanyar Warware Takaddamar Cinikayya Tsakanin Sin Da Amurka

Nazarin CGTN: Jama’ar Duniya Na Ganin Tattaunawa Da Hadin Gwiwa A Matsayin Hanyar Warware Takaddamar Cinikayya Tsakanin Sin Da Amurka

June 7, 2025
Sojojin Sama Sun Tarwatsa Maɓoyar Ƴan Ta’adda, Ya Daƙile Hari Ranar Idi A Borno

Sojojin Sama Sun Tarwatsa Maɓoyar Ƴan Ta’adda, Ya Daƙile Hari Ranar Idi A Borno

June 7, 2025
Amurka

2027: An Yi Kira Ga Masu Mulki Da Su Rungumi Tafarkin Inganta Rayuwar Al’umma

June 7, 2025
Tottenham Ta Raba Gari Da Kocinta Ange Postecoglu

Tottenham Ta Raba Gari Da Kocinta Ange Postecoglu

June 7, 2025
Tufka Da Warwarar INEC Kan Yiwuwar Zaben 2023

Ana Ci Gaba Da Samun Rudani Yayin Da INEC Ta Jinkirta Rajistar Sabbin Jam’iyyu

June 7, 2025
Manchester City Ta Kammala Daukar Tijjani Reijnders Daga AC Milan

Manchester City Ta Kammala Daukar Tijjani Reijnders Daga AC Milan

June 7, 2025
Ban Sa Ran Lashe Kyautar Ballon D’or Ta Bana Ba – Lamine Yamal

Ban Sa Ran Lashe Kyautar Ballon D’or Ta Bana Ba – Lamine Yamal

June 7, 2025
Dangote Ya Sanya Wa Hanya Sunan Tinubu, Zai Kashe Naira Biliyan 900 Don Gina Hanyoyi A Nijeriya

Dangote Ya Sanya Wa Hanya Sunan Tinubu, Zai Kashe Naira Biliyan 900 Don Gina Hanyoyi A Nijeriya

June 7, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.