Dakarun rundunar Sojojin Nijeriya, ta musamman da babban hafsan Sojin ƙasa, Janar Christopher Musa ya tura, ta yi nasarar fatattakar ‘yan ƙungiyar Lakurawa da dama da ke a jahohin Sokoto da Kebbi.
Kwamandan atisayen Fansan Yamma, Manjo Janar Oluyinka Soyele, ne ya bayyana haka ga manema labarai, inda ya ƙara da cewa, rundunar ta lalata sansanoni 22 na ‘yan ta’addan a jihohin.
- Nan Ba Da Jimawa Ba ‘Yan Ta’addan Lakurawa Za Su Zama Tarihi – COAS
- Sojoji Sun Tarwatsa Sansanonin Lakurawa 22, Tare Da Kashe Da Dama A Sakkwato
Ya ce sun yi nasarar ƙwato bindigu hudu, ƙirar PKT 409 7.62mm NATO da harsashi na musamman 94 masu tsahon 7.62mm a yayin fafatawa da ‘yan ƙungiyar ta Lakurawa.
Ya ƙara da cewa an samu nasarorin ne ta hanyar sabbin salon hare-hare da suke kai wa ‘yan bindigar na Lakurawa wanda ya kai ga lalata sansanoninsu.
Soyele ya ci gaba da bayyana cewa an zaɓo dakarun ne tare basu horo na musamman don aikin fatattakar ‘yan ta’addan Lakurawan, inda ya umarce dakarun sojin da su bi ƙa’idojin aiki tare da tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin al’umma yayin bayar da tsoro da ma sauran ayyukansu na yau da kullum.