Wata hazikar ‘yar Nijeriya mai suna Islamiyat Ojelade ta samu gurbin digirk na uku (PhD) a manyan jami’o’in Amurka guda 7 ba tare da yin digiri na farko ko na biyu ba.
Islamiyyat wacce ta sanar da nasararta a LinkedIn ta bayyana cewa ta samu damar samun gurbin karatu a jami’o’in da ke da digiri na uku. Ana ba da takardar shaidar HND a Nijeriya bayan kammala karatun shekaru 4 a manyan Kwalejin Ilimi.
- Kotu Ta Ware 7 Ga Satumba A Matsayin Ranar Fara Shari’a Kan Takardun Bogin Tinubu
- 2023: Dan Yayan Buhari, Fatuhu Muhammed Ya Fice Daga APC
Islamiyat ta samu shaidar kammala HND a fannin fasahar kimiyyar kimiyya a Kwalejin Ilaro, Jihar Ogun, Kudu maso Yamma, Nijeriya.
Ta yi fice sosai daga makarantar inda ta samu maki 3.89, wanda hakan ya sa ta zama mafi hazakae daliban da suka kammala karatun 2018.
Islamiyat ta yi fafutukar wariya da ake wa masu takardar shaidar HND a Nijeriya.
Ta bayyana cewa bayan karatun digirinta na farko, ta rude kan matakin da za ta dauka na gaba. “Na tsorata kan abin da zan yi bayan karatun digirina. Na tattauna game da ‘babban burina’ tare da wasu mutane ciki har da abokai, iyaye da malamana,” kamar yadda ta wallafa a LinkedIn.
Ta lura cewa mutane kadan ne suka shiga don taimaka mata amma a karshe, ta samu tallafin karatu na PhD daga Jami’ar Jihar Florida, Jami’ar Massachusetts Amherst, Jami’ar Kansas, Jami’ar Kentucky, Jami’ar North Texas, Rensselaer Polytechnic. Cibiyar da Jami’ar Marquette a Wisconsin.
Dalibai da dama na samun guraben karatu a kasashen waje, musamman wadanda suke da hazaka sannan suka samu sakamakon jarabawa mai kyau.