Babban Kwanturolan Hukumar Kwastam ta Nijeriya (NCS), Adewale Adeniyi, ya sanar da cewa hukumar ta tattara harajin naira tiriliyan 6,105,315,543,488.50 a karshen shekarar 2024, wanda ya zarce yadda ta yi hasashe N5.079trn da N1,26,245, 677,40
Hukumar ta kuma bayyana cewa, an yi asarar Naira tiriliyan 1.622trn a matsayin rangwame ga ‘yan kasuwa domin bunkasar tattalin arziki da habaka yanayin kasuwanci a karkashin shirin gwamnatin tarayya na cire harajin shigo da wasu kaya daga ketare.
- Gwamnatin Tarayya Ta Tabbatar Da Ɓullar Cutar Murar Tsuntsaye A Kano
- Majalisa Ta Tuhumi JAMB Kan Kashe Biliyan 2 Kan Abinci Da Maganin Sauro
Adeniyi ya bayyana hakan ne a ranar Talata a wani taron manema labarai kan fayyace ayyukan hukumar a shekarar 2024.
Ya ce hukumar kwastam ta yi hada-hadar kudaden kasuwancin shige da fice na kayayyaki na jimillar kudi kimanin Naira tiriliyan 196.94 a shekarar 2024 kadai.
Adeniyi ya ce an samu nasarar hakan ne ta hanyar hada-hadar shigo da kayayyaki guda 1,262,988.
A cewarsa, hukumar Kwastam ta kama kayayyakin da aka yi fasakwari kimanin miliyan 3,555 duk acikin shekarar 2024 wanda darajar kayayyakin ta kai Naira biliyan 28.46