Alummar Masarautar Yauri da ke a kudancin Jihar Kebbi, sun shirya tsaf, domin gudanar da bikin gargajiya na Rigata.
An shafe sama da shekaru 200 ana gudanar da wannan bikin gargajiyar wanda kuma ba a ciki ganin irinsa, a kasar nan ba, saboda ana gudanar da bikin ne, kan tudu da kuma gudanar da wasanni, a kan Kogin Neja.
- Sin Ta Samar Da Yuan Biliyan 6.66 Don Gudanar Da Ayyukan Farfado Da Kauyuka Dake Yankunan Kananan Kabilu
- Kar Ku Tayar Da Hankalinku Kan Cutar Tsuntsaye – Ma’aikatar Lafiya Ta Kano
Kazalika, ana gudanar kade-kade da raye-raye, wasanni a kan kogi da kuma nuna alkarcin fannin aikin noma da Allah ya wadaci Masarautar da su.
Bkin na da nasaba da hudda a tsakanin ‘yan Adam da kuma dabbibin ruwa, kamar Dorinar ruwa, Kada wadanda suke ke kai wa bil Adama hari, tare da janyo mutuwar su.
Domin a dakile wannan barazanar hakan ke sanya wa a duk shekara, jaruman Gungu, suka shiga cikin Kwale-Kwale dauke da makamai sun yi farautar irin wadannan mugayen dabbobin ruwan.
Suna kuma yin hakan ne, domin su samar da tsaro a kan Kogunna da tabbatar da zirga-zirga a cikin sauki da kuma kara habaka sauran hada-hadar kawuanci a Kogunan.
Bayan zuwa Turwan mallaka a karni na 19, an haramta farautar Dorinar ruwa, sai dai, daga baya, an ci gaba da yi a bikin na Rigata, domin a nuna irin karfin da Masarautar take da shi, musamman a lokutan bukukuwan aure.
Kai ziyarar da marigayi Sardaunan Sokoto kuma Firimiyan Arewa Sir Ahmadu Bello, a yankin na Yauri, hakan ya sake farfado da bikin na Rigata, wanda lokacin ziyararsa, aka gudanar da wasanni da kuma baje kolin amfanin gona, domin a karrama shi.
Bisa jajircwar Mai Martaba Sarkin Yauri Dakta Mohammad Zayyanu Abdullahi, CON, da kuma namjin kokarin gwamnan jihar, an sake farfado da bikin karo na 42.
Mayar da hankali da Dakta Nasir Idris da kuma, Kauran Gwandu, Gamjin Yauri, ya taimaka matuka wajen farfado da martabar bikin.
Kazalila, tsarin da Gwamna Idris ya samar na daga darajar yawon bude Ido a jihar, hakan ya kara janyo ra’ayin bunkasar bukukuwan gargajiya a jihar.
Misali, manya bukukuwan gargajiya kamarsu, bikin kamun Kifi na kasa da kasa na Argungu da ake gudanarwa a garin Argungu,bikin gargajiya na the Uhola.
Bikin gargajiya na Zuru da ake yi a yankin Geandu, ya taimaka wajen daga darajar yawon bude Ido na jihar Kebbi a Idon duniya.
Duba da yadda ake gudanar da manyan bukukuwan gargajiya a kasar, sai dai, akwai wasu manyan kalubale nan a ci gaba da gudanar da bukuwan da kuma karancin kudi, musamman domin a ci gaba da gudanar da bukukuwan.
Bukukuwa da dama, sun bace bat, saboda rashin kudin ci gaba da gudanar da su, wasu ma, tun daga matakin farkon fara gudanar da su.
Idan har ana son gudanar da bukukuwan gargajiya su ci gaba da dorewa, dole ne, alumma su bayar da na su goyon bayan, musamman wajen samar da kudade.
Bikin na Rigata, na daga cikin manyan bukuwan da ke a kasar ana kuma gudanar da bikin ne, a duk shekara a cikin watan Fabirairun.
Ana fara gudanar da bikin ne, ta hanyar baje kolin amfanin gona, sai kuma nuna al’adun gargajiya da kade-kade da kuma raye-raye, tare da yin gasar kokawar gargajiya.
A bikin ana gudanar da gasar wasa da Kwale-Kwale a kan Kogi, inda kuma a bikin ya hada da, ‘yan tawagar kai Amarya tare da yi mata rakiya da kade-kade a cikin Jirgin Kwale-Kwalen da aka yi masa ado
A baya, ana yi wa Amaryar rakia ne, zuwa gidan mijinsu a cikin Kwale-Kwale, musamman a yankunan da ake da Rafuka.
A 2023, an karamma Gwamnan jihar Dakta Nasir Idris a wajen bikin na bara da wakar Gambara, wacce ita ce ta farko, da aka fara gabatarwa a lokacin bikin.
A yayin da ake shirye-shiryen gudanar da bkin na bana, ‘yan Nijeriya na ci gaba da sa ido, domin su ga yadda bikin na zai gabatar da wasu sabbin dabaru, musamman a bangaren kade-kade.