• English
  • Business News
Wednesday, September 17, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Najeriya Ta Zama Abokiyar Huldar BRICS

by CGTN Hausa and Sulaiman
8 months ago
in Daga Birnin Sin
0
Najeriya Ta Zama Abokiyar Huldar BRICS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Labarai Masu Nasaba

Har Kullum Burin Sin Shi Ne Wanzar Da Daidaito Da Cimma Moriya Tare Da Amurka

Guterres: Jerin Shawarwarin Da Sin Ta Gabatar Sun Cika Ka’idar Kundin Tsarin Majalisar Dinkin Duniya

A yayin gudanar da aikinta na shugabancin karba-karba na BRICS, gwamnatin Brazil ta sanar a ranar 17 ga Janairun 2025, da amincewa da Najeriya a matsayin abokiyar hadin gwiwar kungiyar ta BRICS. Hakan na nufin Najeriya ta zama kasa ta tara na abokan huldar BRICS, tare da kasashen Belarus, Bolivia, Cuba, Kazakhstan, Malaysia, Thailand, Uganda, da Uzbekistan. Wannan sabon tsarin da aka kirkiro a taron kolin BRICS karo na 16 a Kazan a watan Oktoban 2024 na taka rawar gani wajen karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa da kuma sake fasalin tsarin mulkin duniya. A halin yanzu BRICS tana da cikakkun mambobi 10 da suka hada da Brazil, Rasha, Indiya, Sin, Afirka ta Kudu, Masar, Habasha, Indonesiya, Iran, Hadaddiyar Daular Larabawa yayin da wasu kasashe da dama suke kan hanyarsu ta shiga kungiyar. Kasancewar cikakken mamba na kungiyar na nufin samun damar inganta mu’amalar hada-hadar kudi da sauran kasashe mambobi da samun garkuwa daga mamayar kasashen yammacin duniya, tare da samun damar shiga tsarin manufofi da kudurorin kungiyar wadanda suka ginu a kan hadin gwiwar mutunta juna kuma a gudu tare don a tsira tare.

A matsayinta na abokiyar huldar kungiyar, Najeriya na iya amfani da damar wajen rage dogaro da tasirin dalar Amurka a harkokin da suka shafi hada-hadar kudi tsakaninta da sauran kasashe tare da karfafa yin kasuwanci da kudinta. Hakan kuma zai iya taimaka mata wajen magance matsalolin da ake fuskanta na saye da sayar da kayayyaki, wadanda ke ci gaba da zama manyan ginshikai a cikin matsalar tattalin arzikin kasar. Har ila yau, duk da cewa Najeriya ba cikakkiyar mamba ba ce, za ta iya samun damar samun kudade bisa wasu sharudda na musamman don gudanar da ayyukan samar da ababen more rayuwa da ayyukan raya kasa ta hanyar Sabon Bankin Raya Kasa (NBD) da Contingent Reserve Arrangement (CRA). A cewar wani rahoton Majalisar Kula da Huldar Kasashen Waje (CFR) da aka wallafa a watan Disamba, daya daga cikin manyan manufofin BRICS shi ne yin ayyukan da za su maye gurbin bukatuwar mambobinta zuwa ga Bankin Duniya da Asusun Lamuni na Duniya (IMF). Mambobin BRICS na fatan cewa wannan tsarin ba da lamuni na iya karfafa hadin gwiwar kasashe masu tasowa da kuma rage dogaro ga hanyoyin samar da kudade na gargajiya. (Mohammed Yahaya)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Karon Farko CMG Zai Watsa Shirye-Shiryen Shagalin Murnar Sabuwar Shekara Ta Kasar Sin Ga Mutane Masu Bukata Ta Musamman

Next Post

Sin A Shirye Take Ta Shawo Kan Sabani Tare Da Sabuwar Gwamnatin Amurka

Related

Har Kullum Burin Sin Shi Ne Wanzar Da Daidaito Da Cimma Moriya Tare Da Amurka
Daga Birnin Sin

Har Kullum Burin Sin Shi Ne Wanzar Da Daidaito Da Cimma Moriya Tare Da Amurka

2 hours ago
Guterres: Jerin Shawarwarin Da Sin Ta Gabatar Sun Cika Ka’idar Kundin Tsarin Majalisar Dinkin Duniya
Daga Birnin Sin

Guterres: Jerin Shawarwarin Da Sin Ta Gabatar Sun Cika Ka’idar Kundin Tsarin Majalisar Dinkin Duniya

3 hours ago
Babban Jirgin Ruwan Kasar Sin Ya Nufi Yankin Tekun Kudancin Kasar Domin Gwaji Da Samar Da Horo
Daga Birnin Sin

Babban Jirgin Ruwan Kasar Sin Ya Nufi Yankin Tekun Kudancin Kasar Domin Gwaji Da Samar Da Horo

20 hours ago
Shawarwarin Sin: Ingantattun Hanyoyi Masu Sauki Na Warware Sabani
Daga Birnin Sin

Shawarwarin Sin: Ingantattun Hanyoyi Masu Sauki Na Warware Sabani

21 hours ago
Sin Da Amurka Sun Yi Tattaunawar Keke-da-keke Kan Batutuwan Cinikayya Da Manhajar TikTok
Daga Birnin Sin

Sin Da Amurka Sun Yi Tattaunawar Keke-da-keke Kan Batutuwan Cinikayya Da Manhajar TikTok

22 hours ago
Sin Da Ghana Na Fadada Hadin Gwiwa A Bangaren Ciniki Da Zuba Jari
Daga Birnin Sin

Sin Da Ghana Na Fadada Hadin Gwiwa A Bangaren Ciniki Da Zuba Jari

23 hours ago
Next Post
Sin A Shirye Take Ta Shawo Kan Sabani Tare Da Sabuwar Gwamnatin Amurka

Sin A Shirye Take Ta Shawo Kan Sabani Tare Da Sabuwar Gwamnatin Amurka

LABARAI MASU NASABA

‘Yansanda Sun Kama Mutane 6 Kan Zargin Haƙar Ma’adinai Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Neja

‘Yansanda Sun Kama Mutane 6 Kan Zargin Haƙar Ma’adinai Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Neja

September 17, 2025
Har Kullum Burin Sin Shi Ne Wanzar Da Daidaito Da Cimma Moriya Tare Da Amurka

Har Kullum Burin Sin Shi Ne Wanzar Da Daidaito Da Cimma Moriya Tare Da Amurka

September 17, 2025
Yanzu-yanzu: Shugaba Tinubu Ya Ɗage Dokar Ta-ɓaci A Jihar Ribas

Yanzu-yanzu: Shugaba Tinubu Ya Ɗage Dokar Ta-ɓaci A Jihar Ribas

September 17, 2025
Guterres: Jerin Shawarwarin Da Sin Ta Gabatar Sun Cika Ka’idar Kundin Tsarin Majalisar Dinkin Duniya

Guterres: Jerin Shawarwarin Da Sin Ta Gabatar Sun Cika Ka’idar Kundin Tsarin Majalisar Dinkin Duniya

September 17, 2025
NECO Ta Saki Sakamakon Jarrabawar 2025

NECO Ta Saki Sakamakon Jarrabawar 2025

September 17, 2025
Lakurawa Sun Hallaka Jami’in Kwastam A Jihar Kebbi

Lakurawa Sun Hallaka Jami’in Kwastam A Jihar Kebbi

September 17, 2025
Sojoji Sun Kashe Mayaƙan ISWAP 11 A Borno Da Adamawa

Sojoji Sun Kashe Mayaƙan ISWAP 11 A Borno Da Adamawa

September 17, 2025
‘Yan Bindiga Sun Sace Mutum 7 A Jihar Neja

‘Yansanda Sun Kama ‘Yan Ƙungiyar Asiri Da Ɓarayin Kifi A Jihar Neja

September 17, 2025
Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC Na Nasarawa, Aliyu Barde, Ya Rasu

Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC Na Nasarawa, Aliyu Barde, Ya Rasu

September 17, 2025
Sowore Ya Maka DSS, Meta da X A Kotu Kan Take Masa Haƙƙi

Sowore Ya Maka DSS, Meta da X A Kotu Kan Take Masa Haƙƙi

September 17, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.