Jami’ai daga sassan kasar Sin da na kungiyar tarayyar Afirka ta AU, sun bayyana tarin nasarori da aka cimma, a fannonin diflomasiyya da tattalin arziki, yayin da suke zurfafa hadin gwiwa a harkokin kasa da kasa da na shiyyoyi.
Jami’an sun yi bayanan ne jiya Litinin, a sabuwar farfajiyar ginin ofishin wakilcin kasar Sin a kungiyar AU dake birnin Addis Ababa fadar mulkin Habasha, lokacin da aka gudanar da liyafar murnar zagayowar bikin bazara na sabuwar shekarar gargajiya ta kasar Sin.
- Fashewar Tankar Mai A Suleja: An Kai Mutum 20 Manyan Asibitocin Abuja Don Samun Kulawa Ta Musamman
- Tsakanin Nijeriya Da BRICS+: Idan Zamani Ya Dinka Riga…
A bana bikin bazara ya fado ranar 29 ga watan Janairun nan, inda za a shiga shekarar Maciji bisa lissafin watannin kalandar gargajiya ta kasar Sin.
Da yake tsokaci game da hakan, shugaban ofishin wakilcin kasar Sin a kungiyar AU Hu Changchun, ya ce gwamnatin kasar Sin ta himmatu wajen aiki tare da kasashen Afirka, wajen aiwatar da sakamakon da aka cimma yayin dandalin tattauna hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka na FOCAC a birnin Beijing, da aiwatar da ayyukan hadin kai 10 da aka sanar, da aiki tare kan turbar zamanantarwa.
A nata bangare kuwa, mataimakiyar shugaban hukumar zartarwa ta kungiyar AU Monique Nsanzabaganwa, cewa ta yi hadin gwiwar AU da Sin, ya haifar da nasarori da alfanu mai tarin yawa a shekarun da suka gabata. Ta ce har kullum, Sin tana yin tsayin daka wajen goyon bayan fafutukar kasashen Afirka na yaki da mulkin mallaka, da siyasar nuna fin karfi da nuna wariyar launin fata, wanda kungiyar ke matukar godiya kan hakan. (Saminu Alhassan)