A ranar Litinin ne gwamnatin Nijeriya ta hannun hukumar sadarwa ta (NCC) ta duba koken kamfanonin sadarwar, inda ta amince musu da su yi ƙarin kuɗin kira da sayen data da kashi 50 cikin 100 sabanin abinda suka bukata.
A kwanakin nan Kamfanonin sadarwa a Nijeriya, ƙarƙashin jagorancin Shugaban hukumar gudanarwar kamfanin MTN, Karl Toriola, sun buƙaci amincewar gwamnatin tarayya kan su yi ƙarin kashi 100 bisa 100 na kuɗin kiran waya da data.
- Xi Jinping Ya Gana Da Shugaban Rasha Ta Kafar Bidiyo
- Matatar Dangote Ta Bai Wa Ɗalibai 473 Tallafin Karatu
Dalilinsu na neman wannan ƙarin, shi ne tsadar rayuwa, wanda ya ce kamfanin sadarwa a Nijeriya na fuskantar barazanar durƙushewa a sakamakon yadda farashin komai ya yi tashin gauron-zabi kama daga farashin man fetur da farashin kuɗin wuta da sauransu.
A cewar Karl Toriola, a halin yanzu ba batun riba suke ba, sai dai yadda za su ci gaba da kasuwanci, ko a kwanakin baya kungiyar kamfanonin sadarwa ta yi barazanar za a iya samun katsewar sabis ɗin waya a wasu sassa na ƙasar muddin ƙarin bai tabbata ba.
Hakan na nufin za a iya samun tangarɗa a fannoni daban-daban da suka shafi tsaro da kiwon lafiya da ilimi da harkokin kasuwanci da sauran al’amuran yau da kullum, kasancewar irin tasirin da kafafen sadarwa ke da shi a rayuwar al’umma.
Wannan ta ƙaddamar ƙarin dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da ‘yan Nijeriya ke ci gaba da kokawa game da hauhawar farashi a sakamakon wasu tsare-tsaren gwamnatin Nijeriya, wanda ake alaƙanta su da cire tallafin man fetur.
Shugaban ƙungiyar masu amfani da layukan sadarwa ta NATCOMS, Deolu Ogunbanjo, ya ce hukumar NCC ba ta tuntuɓesu ba game da ƙarin kashi 50 ciki 100 na farashin kuɗin waya da datan da ta yi.
A cewarsa suna sane da ƙalubalen da kamfanonin sadarwa ke fuskanta, tare da bayar da shawarar ƙarin kashi 5 ko 10 cikin 100, ya kuma shaida cewa matakin NCC na ƙarin abu ne da ba za su lamunta ba, inda ya sha alwashin ƙalubalantar ƙarin ƙudin a gaban kotu.