Gwamnan jihar Ribas da ke Kudu maso Kudancin Nijeriya Nyesom Wike ya ce bai kai karar dan takarar shugabancin kasar na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da da gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal kotu ba.
BBC ta rawaito cewa, Wike ya bayyana hakan ne yau Juma’a a wani wajen taro da manyan jam’iyyar a birnin Port Harcourt.
- Zaben Fidda Gwanin PDP: Wike Ya Gurfanar Da Atiku, Tambuwal Da INEC A Gaban Kotu
- Gwamna Wike Ya Karyata Cire Tutocin PDP Daga Gidan Gwamnatin Jihar Ribas
Ya kara da cewa bai ba wa kowa izinin kai ƙararsu kotu ba.
Tun da fari, wasu jaridun kasar sun rawaito cewa Wike da wani ƙusa a PDP mai suna Newgent Ekamon sun shigar da ƙara mai lamba FHC/ABJ/CS/782/2022 da ke kalubalantar janyewar Tambuwal daga zaɓen fitar da gwani da kuma goyon bayan Atiku.