Kamar yadda aka sani ne, NAHCON ce ke da alhakin shiryawa tare da gudanar da ayyukan da suka shafi aikin hajji a kasar nan, wanda kuma ita ce ke da alhakin ganin aikin ya gudana ba tare da wata tangarda ba.
Kamar kowace shekara, a bana ma Hukumar ta yi wannan aiki, inda kuma aka samu nasarori masu yawan gaske. Haka kuma, babu yadda za a yi a ce an yi wannan aiki ba tare wata matsala ba.
- Shugaba Buhari Zai Kawo Karshen Rashin Tsaro A Nijeriya -Buratai
- Ziyarar Babbar jami’ar Lithuania A Taiwan Shirme Ne
Game da korafin da wasu ke yi na cewa an bar wasu maniyyata a kasa ba su samu tafiya aikin hajjin ba, wannan ba abin korafi ba ne domin Hukumar ta sha bayyana cewa ba duk wanda ya biya kudinsa ne zai samu tafiya ba, don haka ne ma ake fada ma jama’a don su zama cikin shiri.
Saboda haka ga duk mai bibiyar aikin Hajji a duk shekara, sam wannan ba abu ne da ya kamata ya zama abin korafi ba, musamman bisa la’akari da yadda ita kanta Hukumar kasar Sadiyya ta ke rage yawan maniyyatan a duk shekara.
Wani abu mai daure kai kuma shi ne yadda ake samun korafi daga wasu ma’aikatan Hukumar wadanda ba su samu damar zuwa kasar mai tsarki don gudanar ayyukan da aka saba ba, alhali a bayyana ya ke, cewa ba duk ma’aikatan ne za a dade a tafi ba, dole akwai wadanda za a bari a ofis don wasu ayyukan.
Bugu da kari, duk wani ma’aikacin da bai samu nasarar tafiya aikin hajjin ba, to akwai wani dan ihsani da ake yi masu a zaman da suke yi a kasar nan.
Amma sai ya zama duk da irin kyakkyawan tsarin da ake da shi wajen zabar ma’aikatan da za su tafi aikin hajjin, abin takaci, sai ya zama wasu suna fusata, har suna shiga kafafen yada labarai sun yin wadansu zarge-zarge marasa tushe.
Haka kuma, rikici ko rashin jituwar da kan faru tsakanin Hukumomin kula da jin dadin Alhazai na jihohi na daga cikin abubuwan da kan kawo tsaiko a harkar jigilar maniyyatan.
Wani babban misali, shi ne irin wanda aka samu tsakanin jihar Kano da kamfanin jirage na Azaman air, da kuma tsakanin jihar Kanon dai da adashen gata, alhali ita NAHCON ta riga ta yi kyakkyawan shiri a kan haka, wanda hakan ya kawo matsaloli.
Saboda haka ga duk wanda ya san irin namijin kokarin da NAHCON ke yi wajen ganin an samu aikin hajji mai cike da nasara, to ba zai damu da wasu kananan maganganu da wasu masu son zuciya ke yi ba.
Ina ganin bisa kyawawan tsare-tsaren da hukumar nan ke yi a duk shekara, to lallai ta cancanci jinjina ne ta musamman, musamman a ‘yan shekarun nan da suka gabata, wanda hakan ya sa suke samun lambar yabo bisa hukumar da ta yi fice wajen iya gabatar da tsari a aikin hajjin.