A ranar 31 ga watan Yuli ne, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bayyana kammala rajistar mallakar katin zabe da ta bude a ranar 28 ga Yunin 2020, shekara biyu kenan da wata guda.
Bayan kammala rajistar, hukumar ta ce ta yi sabbin rajista ga ‘yan Nijeriya miliyan 12, 298, 944. Kafin nan akwai masu rajista har mutum 84, 000, 484.
- Shugaba Buhari Zai Kawo Karshen Rashin Tsaro A Nijeriya -Buratai
- Ziyarar Babbar jami’ar Lithuania A Taiwan Shirme Ne
Wato a yanzu akwai wadanda suka mallaki katin zabe har miliyan 96, 299, 428 kenan.
A bayanan da hukumar INEC ta fitar har yanzu Kano da Legas ke da mafi yawan masu rajista.
Jihohi uku da ke kan gaba wajen yawan wadanda suka yi rajista kwanan nan, sun hada da Legas da ke da mutum 585,629.
Sai Kano mai 569, 103. Ta uku it ace Jihar Delta mai mutum 523, 517. Jihohi masu karancin wadanda suka yi rajista kwanan nan su ne: Ekiti da ke da mutum 124, 844.
Mai bi mata ita ce Jihar Yobe mai mutum 152, 414. Sai Babban Birnin Tarayya (FCT), Abuja mai mutum 211, 341.
A wannan kididdigan ya nuna cewa yankin Kudu sun fi yankin Arewa karin masu rajistar, alamu na kuma nuna cewa kowani bangare zai iya yin dan bangarensa ne a zaben 2023.
Amma dai ba a nan gizo ke sakar ba, daga bibiyar yawan masu rajistar zabe, za a fahimci ‘yan takarar jam’iyyar APC da PDP har yanzu su ne a sahun gaban wajen yiwuwar lashe zabe.
Amma fa karfin yunkurowar da Kwankwaso na NNPP da Obi na LP za su iya kawo wa nasarar Atiku cikas sosai.
Haka kuma za su iya hana Tinubu lashe zabe kaitsaye. Sakamakon zaben Ekiti da Osun na gwamna da kuma zabukan cike gurbi na jihohi da tarayya sun nuna APC da PDP dai ne manyan ‘yan takara.
Idan a bi ta barawo, to a bi ta ma bi sahu, kamar yadda masu iya magana suke cewa tun bayan kafuwar jam’iyyar NNPP mai kayan marmari na Kwankwas, gaba daya tasirin jam’iyyar PDP ya mutu a Kano.
Ita kanta jam’iyya mai mulki a Kano ta kasa tsayuwa da kafafuwanta don ta shiga rudani har wasu jiga-jiganta suka shiga NNPP irin su Malam Ibrahim Shekarau, Sanata kuma Tsohon Gwamna a jihar.
Kasancewar a duk arewacin Nijeriya, Jihar Kano ce aka fi samun yawan kuri’u, kenan akwai yiwuwar Kwankwaso zai iya yi wa duk wata jam’iyya illa a jihar.
Masu sharhi kan siyasa sun hasaso cewa duk dan takarar da bai samu nasara a jihohin Kano ko Legas ko Kaduna ba, ko shakka babu zai wahala ya iya samun nasara a zaben 2023 na shugaban kasa.
A Kaduna ma nan ana ganin Gwamna Nasir El-Rufai ya janyo wa jam’iyyar APC bakin jini. Sannan kuma dan Jihar Kaduna ne mataimakin takarar Peter Obi na jam’iyyarr LP; wato Yusuf Datti Baba-Ahmed, ko ba komai a jihar LP za ta iya jan wasu kaso na kuri’u da za a jefa.
Idan aka koma kudu maso kudu kuwa, sanin kowa ne jam’iyyar APC ba ta da wani tasiri a yankin. Mutanen yankin sun so a ce Gwamna Wike ne dan takarar PDP ba Atiku Abubakar ba.
Dalili kenan PDP ta kasa barci tana so sai ta lallashi Gwamna Nysome Wike daga fushin da ya yi. Dama kuma yankin na PDP ne tun filazal.
Haka kuma rashin bai wa dan kudu maso gabas takara da PDP ko APC suka yi, ya sa jihohin Igbo sun karkata ga dansu Peter Obi na jam’iyyar LP.
Idan kuwa aka koma ma’anar siyasa za a ga cewa, siyasa hanya ce da mutane ke bi wajen rayuwa a hade, ko a tare ko a kungiyance cikin manufa daya.
Siyasa na nufin hada yarjejeniya tsakanin mutane domin su zauna tare duk da mabam-bantan ra’ayoyi, kabilu da addinai, a birane da kasashe.
Bisa wannan ta’arifin na siyasa a yanayin da ake tafiya a Nijeriya, kowani bangare ko yanki nasu suke yi.
Kenan yankin kudu sun yunkuro a wannan karo ta la’akari da samun yawan masu rajistan katin zabe. Da can sun san yankin arewa ba yinsu suke yi ba.
Kuma a yanzu yankin arewa za a yi masu illa game da rarrabuwan ‘yan takara da aka samu a yankin. Ko ma dai mene ne, Hausawa na cewa ‘ba a san ma ci tuwo ba, sai miya ta kare’.