Akalla mutanen Indiya kimanin 100 da ake zargin sun shiga Amurka ta barauniyar hanya ne ake sa ran za su isa Jihar Punjab a yau.
Wani jirgin saman sojojin Amurka da ke dauke da mutanen ya bar birnin Tedas a daren ranar Talata.
Jami’ai a birnin Amritsar sun bayyana cewa a shirye su ke na karbar mutanen.
Donald Trump ya sanya aikin korar dubban bakin haure da ke zama a Amurka ba bisa ka’ida ba cikin muhimman tsare tsarensa.
Ya ce Firaministan Indiya Narendra Modi ya tabbatar masa cewa kasarsa za ta yi ‘abin da ya dace’ wajen karbar wadanda za a dawo da su.