Gwamnan Jihar Filato, Barr. Caleb Mutfwang, ya nuna matuƙar damuwa kan yawaitar daina makaranta a yankunan da ake haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba. Ya ce bincike ya nuna cewa yawan ɗaliban da ke shiga makaranta ya ragu sosai a Bassa, Riyom, Jos ta Kudu, da Barkin Ladi, lamarin da ke barazana ga makomar matasa da ci gaban jihar gaba daya.
A cewarsa, gwamnati ta ƙaddamar da samame a wuraren haƙar ma’adanai domin daƙile wannan matsala, yana mai jaddada cewa ba hana jama’a neman abinci ake yi ba, amma ana ƙoƙarin kare rayuwa da makomar yara. Mutfwang ya ce sun gano cewa wasu iyaye a Bassa na tura ‘ya’yansu yin aikin ƙarfi maimakon zuwa makaranta, kuma gwamnati na bin diddigin lamarin.
- Annobar Cutar Murar Tsuntsaye Ta Yadu A Jihohin Filato Da Katsina
- Gobara Ta Yi Sanadiyar Asarar Miliyoyin Dukiya A Kasuwar Katako Da Ke Jos
Gwamnan ya buƙaci shugabannin al’umma da na addini su haɗa kai da gwamnati wajen wayar da kan jama’a kan illolin haƙar ma’adanai da yadda take haddasa barin makaranta. Ya ce za a fara gangamin wayar da kai tare da cibiyoyin addini don faɗakar da iyaye kan mahimmancin ilimi.
Dangane da matsalar tsaro, Mutfwang ya ce gwamnatinsa ba za ta amince da duk wani yunƙuri na tada zaune tsaye ba. Ya jaddada cewa mutanen Filato na da karimci, amma suna buƙatar a girmama dokokinsu da al’adunsu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp