Marco Rubio, a ranar Talata ya ce Amurka tana kokarin ganin an samu mafitar adala mai dorewa wajen kawo karshen yakin da Rasha ta shafe kimanin shekaru uku ta na yi a Yukiren, sai dai dole ne Rashar da Yukiren, kowaccen su, ta hakura da wani abu, kafin a iya cimma zaman lafiya.
Manyan jami’an Amurka da Rasha sun kamala tattauwar sulhun da suka yi a birnin Riyadh na kasar Saudiyya a ranar Talata, inda suka tattauna akan samo mafita ga yakin Yukiren, kwanaki gabanin sarki mai jiran gado, Yarima Muhammad ibn Salman ya kira wani taro da shugabannin Misra, Jordan,katar da Hadaddiyar Daular Larabawa su tattauna akan martanin kasashen Larabawa ga alkawrin da shugaban Amurka Donald Trump ya yi cewa zai karbe ikon Gaza.
- Kalaman Trump Marasa Kan-gado Game Da Gaza Za Su Kara Tsananta Halin Da Ake Ciki A Gabas Ta tsakiya
- Trump Na Son Karbe Ikon Gaza Domin Sauya Wa Falasdinawa Matsuguni
Tattaunawar 2 da basu da alaka, ya nuna irin rawar da yariman take takawa a yunkurin ganin Trump ya cika alkawarin da ya yi wa magoya bayansa a lokacin gangamin yakin neman zabe na kawo karshen yakin Yukiren da na Gaza.
Shugaba Trump ya sake bayyana cewa zai gaggauta kawo karshen yakin.
Rubio ya yi wannan bayanin ne, bayan da shi da sauran manyan jami’an Amurka su ka gana ta tsawon sama da sa’o’i hudu a kasar Saudiyya da Ministan Harkokin Wajen Rasha, Sergy Labrob da hadimansa, a wani yunkurin farko na kawo karshen yakin, da kuma inganta dangantakar Amurka da Rasha da ta yi tsami.
Manufar ita ce a kawo karshen wannan tashin hankalin ta hanyar adalci, mai dorewa, wace dukkanin bangarorin da abin ya shafa za su aminta da ita” in ji Rubio ga menema labarai, duk da cewa babu jami’an Yukiren ko na Turai a wurin tattaunawar.
A wani labarin kuma, shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa ya shaida wa Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio cewa kasarsa ba za ta amince da korar Falasdinawa daga Gaza ba.
Mohammed bin Zayed Al Nahyan na mayar da martani ne ga shirin Shugaba Trump na Amurka na karbe ikon Zirin bayan sauya wa al’ummar Gaza matsuguni.
Shugaban na Hadaddiyar Daular Larabawa ya ce sake ginin Gaza abu ne da ya kamata a hada shi da shirin da zai samar da zaman lafiya.
A ci gaba da rangadin da Marco Rubio yake a Gabas ta Tsakiya tuni ya je Isra’ila da Sudiyya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp