Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta bayyana cewa mutane bakwai sun rasa rayukansu a gobara daban-daban da suka afku a jihar cikin watan Fabrairu 2025. Rahoton ya kuma nuna cewa an samu tashin gobara 77, an gudanar da ceto 11, yayin da aka samu ƙarar bogar bogi guda uku a cikin wannan lokaci.
Sanarwar da Kabiru Isah Jaafar ya fitar a madadin jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Saminu Yusif Abdullahi, ta bayyana cewa kadarori da darajarsu ta kai naira miliyan 50.3 sun lalace sakamakon gobara, yayin da aka ceto wasu kayayyaki da darajarsu ta kai naira miliyan 180.3. Haka kuma, an ceto rayuwa mutane bakwai da daga gobarar.
- Sabon Kwamishinan ‘Yansanda Ya Kama Aiki A Kano
- ‘Yansanda Sun Kashe Ƙasurgumin Ɗan Bindiga, Dogo Saleh, A Abuja
Hukumar ƙarƙashin jagorancin Alhaji Sani Anas ta shawarci al’umma da su kula da amfani da wuta domin guje wa afkuwar gobara. Haka nan, an yi kira ga direbobi da su bi dokokin hanya, musamman a manyan tituna, don rage afkuwar haɗura da kare rayuka da dukiyoyi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp