إياك نستعينُ : أَي نطلبُ العَونَ مِنْكَ عَلَى الْعِبَادَةِ وَ عَلَى جَمِيْعِ أُمُوْرِنَا
Fassara:
“Kuma Kai kaɗai muke neman taimakonka:wato a wurinka kaɗai muke neman taimako a bisa bauta Maka Kai ɗai, kuma a wurinka kaɗai muke neman taimako a kan al’ummammu baki ɗaya” Duba Kitãbu at-Tashīlu Li’ulūmi at-Tanzil [1/33]
Fashin Baƙi:
Kalmar “nasta’īn” tana nufin neman taimako da dogaro da Allah. Wannan yana da nasaba da Tauhīdur-Rubūbiyya, da kuma Tauhidul-Uluhiyya, wato tauhidin da yake tabbatar da cewa Allah ne kaɗai ke gudanar da al’amuran duniya da halittunsa, da kuma tauhidin da yake nuna Allah kaɗai ne ya cancanta a bauta wa Shi kaɗai.
Neman taimako daga Allah yana da nau’i biyu:
1. Taimako na Gaba ɗaya: Wannan yana nufin cewa dukkan halittu suna buƙatar Allah wajen gudanar da rayuwa, kamar samun arziki, da lafiya, da tsira da kulawa, da sauran su.
2. Taimako na Musamman: Wannan kuwa shi ne neman taimako daga Allah wajen yi Masa ibada da biyayya, da bin hanyoyin shiriya, da tabbatar da zuciya a bisa tafarkin daidai har lokacin mutuwa da sauran su.
A wurin Allah kaɗai ake neman taimako a cikin ibada. Wannan yana nuna cewa ibada ba za ta cika ba sai da taimakon Allah. Idan mutum yana son ya yi salla, ko azumi, ko wani aikin addini, to dole ne ya dogara ga Allah domin samun dacewa. Neman taimako daga wanin Allah a cikin lamuran da mutum ba zai iya yi ba sai Allah ya taimake shi, yana cikin shirka. Misali: idan mutum yana kiran matattu ko aljannu don su taimake shi, wannan yana cikin shirka. Amma ana iya neman taimako daga mutane a cikin abubuwan da suke iya yi. Misali, mutum yana iya tambayar wani mutum don ya koya masa ilimi ko ya ba shi kuɗi a matsayin aro, amma dole ne ya yarda cewa Allah ne yake sarrafa komai.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp