An shiga sabon ƙadami a rikicin siyasa da ya turnuƙe Jihar Ribas, inda ƴan majalisar dokokin jihar suka aika wa Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa, Farfesa Ngozi Odu, takardar ƙorafi kan laifuka da suka ce sun aikata.
Ƴan majalisar 26 ne suka saka hannu a takardar, suna masu cewa sun dogara da sashe na 188 na kundin tsarin mulkin Nijeriya na 1999 wajen ɗaukar matakin.
A cewar takardar, ana zargin Fubara da:
- Kashe kuɗin gwamnati ba bisa ƙa’ida ba
- Kawo cikas ga ayyukan majalisa
- Naɗa jami’an gwamnati ba tare da tantancewa ba
- Riƙe albashin ƴan majalisa da na magatakardan majalisa
Haka kuma, ana zargin mataimakiyar gwamna, Farfesa Ngozi Odu, da goyon bayan naɗin mutane kan muƙamai ba bisa ƙa’ida ba.
Shugaban majalisar, Martin Amaewhue, ya bayyana cewa gwamna na da kwanaki 14 don yin martani.
Ya zuwa yanzu dai, Gwamna Fubara bai ce komai ba kan lamarin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp