• English
  • Business News
Friday, October 10, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gidauniyar Dangote Ta Bai Wa Jihar Bauchi Tallafin Buhun shinkafa 25,000

by Sulaiman
7 months ago
Dangote

Gidauniyar Aliko Dangote ta bayar da tallafin buhunan shinkafa guda dubu ashirin da biyar (25,000) mai nauyin kilogiram 10 da aka rabar wa al’umma a ƙananan hukumomi 20 na jihar Bauchi da masallatai da cocina.

 

Babban manajan sashin kamfanonin Dangote, Ahmed Hashim ne ya miƙa buhunan shinkafar a madadin gidauniyar ga gwamnatin jihar Bauchi, inda aka rabar da shi a ranar Talata ga mabuƙata, ya shaida cewar a shekarar da ta gabata ma gidauniyar ta yi irin wannan rabon a faɗin ƙasar nan.

  • Sin Na Adawa Da Haramta Amfani Da DeepSeek Da Gwamnatin Amurka Ta Yi
  • Trump Zai Tattauna Da Putin Kan Kawo Ƙarshen Yaƙin Ukraine

Hashim, ya ce, “A kowace shekara cikin wata Ramadana mai albarka, muna ƙoƙarin tallafawa da kayan abinci ga marasa galihu da marasa ƙarfi a cikin al’umma ta hannun gidauniyar Dangote.

 

LABARAI MASU NASABA

Ƴansanda Sun Ceto Mutane Uku Da Aka Sace A Kano

Matsalar Tsaro: Tinubu Ya Karyata Batun Yi Wa Kiristoci Kisan Ƙare Dangi

“Wannan shi ne karo na biyu, a shekarar da ta gabata dukkanin ƙananan hukumomi a Nijeriya ta hannun jihohinsu sun samu tallafin buhun shinkafa miliyan ɗaya mai nauyin kilogiram 10. Don haka, a wannan shekarar ma muna sake yin makamancin na bara.”

 

Hashim ya yi tilawar cewa gidauniyar Dangote ta himmatu wajen samar da tallafin kayan abinci ga mabuƙata, tallafi a ɓangaren kiwon lafiya, gina ɗakunan kwanan ɗalibai a jami’o’i, da sauran tallafi ciki har da wanda gidauniyar ta yi a lokacin annobar Korona.

 

Ya ce tallafin dafawa ne kan ƙoƙarin da gwamnatocin jihohi ke yi wa al’ummarsu, ya yi fatan cewa shinkafar da suka kawo Bauchi ɗin za ta je kai tsaye ga waɗanda aka bayar domin su wato marasa ƙarfi da marasa galihu a cikin al’umma.

 

Da ta ke amsar tallafin haɗi da ƙaddamar da rabarwa, Kwamishiniyar ma’aikatar kula da harkokin jin ƙai ta jihar, Hon. Hajara Yakubu Wanka ta nuna matuƙar godiyarsu ga gidauniyar Dangote bisa ga wannan tallafin.

 

Ta ce, a daidai lokacin da suke ƙoƙarin kammala rabon tallafin azumin da gwamnan jihar Bala Muhammad ke yi ne suka samu wannan tallafin daga wajen Dangote, don haka ne ta ce hakan zai ƙara kyautata jin daɗin jama’a a irin wannan watan da jama’a ke fama da azumi.

 

A cewar ta, cikin adadin buhu 25,000 da gidauniyar ta kawo Bauchi, za a rabar da guda 500 ga kowace ƙaramar hukuma daga cikin su 20, sai kuma guda dubu 10 da aka ware domin rabarwa a masallatai da cocina, gami da sauran guda 5,000 da za a rabar ga sauran masu ruwa da tsaki.

 

Shi ma a jawabinsa a madadin ƙananan hukumomin jihar Bauchi kuma shugaban ALGON na jihar, Hon. Mahmood Baba Ma’aji ya fara ne da gode wa gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad a bisa tallafin da ya rabar ga ƙananan hukumomin jihar.

 

Hon. Ma’aji ya ce a satukan da suka wuce ne gwamnan ya ƙaddamar da rabon tallafin azumin wanda kowace ƙaramar hukuma sai da ta ci gajiyar hakan.

 

A gefe guda, ya gode wa gidauniyar Dangote bisa ƙara samar da tallafi a jihar ya bada tabbacin cewa za su sanya ido wajen rabon kayan tare da tabbatar da cewa a waɗanda suka dace su ci gajiyar tallafin ne suka amfana.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Ƴansanda Sun Ceto Mutane Uku Da Aka Sace A Kano
Manyan Labarai

Ƴansanda Sun Ceto Mutane Uku Da Aka Sace A Kano

October 10, 2025
Matsalar Tsaro: Tinubu Ya Karyata Batun Yi Wa Kiristoci Kisan Ƙare Dangi
Manyan Labarai

Matsalar Tsaro: Tinubu Ya Karyata Batun Yi Wa Kiristoci Kisan Ƙare Dangi

October 10, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Zaɓi Farfesa Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC 
Manyan Labarai

Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Zaɓi Farfesa Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC 

October 9, 2025
Next Post
Wakilin Musamman Na Shugaba Xi Zai Halarci Bikin Rantsar Da Shugabar Namibiya

Wakilin Musamman Na Shugaba Xi Zai Halarci Bikin Rantsar Da Shugabar Namibiya

LABARAI MASU NASABA

Xi Ya Taya Kim Jong Un Murnar Cikar Jam’iyyar WPK Shekaru 80 Da Kafuwa

Xi Ya Taya Kim Jong Un Murnar Cikar Jam’iyyar WPK Shekaru 80 Da Kafuwa

October 10, 2025
An Zuba Jarin Dala Biliyan 5.2, An Sa Hannu Kan Yarjejeniyoyi 47 A Taron Tattalin Arziƙin Bauchi 

An Zuba Jarin Dala Biliyan 5.2, An Sa Hannu Kan Yarjejeniyoyi 47 A Taron Tattalin Arziƙin Bauchi 

October 10, 2025
Nijeriya

Haramcin Haƙar Ma’adanai: Majalisa Za Ta Kawo Ƙarshen Asarar Dala Biliyan 9 Duk Shekara

October 10, 2025
Ƴansanda Sun Ceto Mutane Uku Da Aka Sace A Kano

Ƴansanda Sun Ceto Mutane Uku Da Aka Sace A Kano

October 10, 2025
Yadda Rashin Isassun Malaman Turanci Da Lissafi Ke Shafar Ingancin Ilimi A Nijeriya (3)

Yadda Za A Magance Yawaitar Malaman Da Ba Su Cancanta Ba A Nijeriya – TRCN

October 10, 2025
Gwamnatin Katsina Ta Rufe Makarantu 32 Masu Zaman Kansu Da Ba Su Da Lasisi

Gwamnatin Katsina Ta Rufe Makarantu 32 Masu Zaman Kansu Da Ba Su Da Lasisi

October 10, 2025
Dangote

Burin ‘Yan Nijeriya Bai Cika Ba Tun Bayan Samun ‘Yancin Kai

October 10, 2025
Matatar dangote

ACF Ta Yi Zargin Shiri Na Musamman Don Rusa Matatar Man Dangote

October 10, 2025
Yadda Zargin Takardar Karatun Bogi Ta Tilasta Wa Minista Nnaji Murabus

Yadda Zargin Takardar Karatun Bogi Ta Tilasta Wa Minista Nnaji Murabus

October 10, 2025
Gwamnatin Kogi Ta Yaba Wa Tinubu Kan Naɗin Amupitan Shugaban INEC

Gwamnatin Kogi Ta Yaba Wa Tinubu Kan Naɗin Amupitan Shugaban INEC

October 10, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.