Kwamandan dakarun RSF na Sudan Mohamed Hamdan Dagalo, ya tabbatar da cewa dakarunsa sun janye daga Khartoum, daya daga cikin manyan biranen Sudan, inda ya yi kira da su sake haduwa a Omdurman, wanda shi ma ke cikin manyan biranen kasar 3.
Cikin wani sakon murya da ya karade kafar Telegram, Mohamed Dagalo ya shaida wa dakarunsa cewa, janyewar wani mataki ne da rundunarsu da tsarin ayyuka suka amince da shi, yana mai ikirarin cewa wani vangare ne na fadada dabarun yaki.
- Koch Usman Abdullahi Zai Jagoranci Kano Pillars A Karon Farko Bayan Dakatarwa
- EFCC Ta Kama ‘Yan China 4, Da Wasu Mutum 27 Kan Zargin Hakar Ma’adinai Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Jos
Ya ce yana tabbatar da cewa sun bar Khartoum, amma za su koma da karin karfi. Ya kara da cewa, har yanzu yakin da aka kusan shafe shekaru 2 ana yi da dakarun gwamnatin Sudan, yana mataki na farko-farko.
Kalaman nasa su ne martani na farko da RSF ta yi kai tsaye ga ikirarin sojin gwamnatin Sudan na baya bayan nan cewa, a ranar 21 ga watan Maris, sun kwace iko da muhimman wuraren dake Khartoum, ciki har da fadar shugaban kasa da gine-ginen gwamnatin tsakiya.
A ranar 26 ga watan Maris, rundunar sojin Sudan ta sake kwace iko da filin jirgin sama na Khartoum, wani muhimmin wuri dake karkashin ikon RSF tun watan Afrilun 2023. A makon da ya gabata ne rundunar sojin kasar ta tabbatar da cewa, ita ce ke iko da dukkanin birnin na Khartoum, daya daga cikin birane uku dake zaman fadar mulkin kasar, baya ga Omdurman da Bahri.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp