Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sadaukar da lambar yabonsa ta ‘Gwarzon Gwamna ta jaridar LEADERSHIP’ ga yara marasa galihu a yankunan karkara.
Ya ce kyautar za ta ƙara masa ƙwarin gwiwa wajen ci gaba da kyautata harkar ilimi.
- Ya Kamata Lambar Yabo Ta Zama Hanyar Ƙarfafa Mana Gwuiwa – Misis Nda-Isaiah
- An Buɗe Sabbin Cibiyoyin Kula Da Masu Cutar Sankarau A Jihohi 6
“Za mu ci gaba da jajircewa wajen bayar da ilimi kyauta da samar da duk kayan da ɗalibai ke buƙata, musamman a yankunan karkara,” in ji Gwamna Yusuf a wajen bikin bayar da kyautar a Abuja.
Gwamnan ya ƙara da cewa wannan karramawar za ta zaburar da sauran masu riƙe da muƙaman gwamnati su mayar da hankali kan jin daɗin al’umma da gina dimokuraɗiyya mai inganci.
“Wannan kyauta ba tawa ce ni kaɗai ba, ta dukkanin yaran Kano ce da ke da burin zuwa makaranta. Wannan yana ƙara mana ƙwarin gwiwa mu ci gaba da ƙoƙari,” in ji shi.
LEADERSHIP tana karrama mutane da ƙungiyoyin da suka taka rawar gani a fannoni daban-daban kamar gwamnati, kasuwanci da al’umma.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp