Mutane biyu ‘yan asalin Jihar Kano sun rasa rayukansu bayan da dutse ya rufta musu a wajen haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba da ke unguwar Farin-Doki a ƙaramar hukumar Shiroro, a Jihar Neja.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 8 na safiyar ranar Lahadi, 13 ga watan Afrilu, 2025.
- Yaƙin Neman Zaɓe A 2027: Ƙungiya Ta Nemi A Maye Gurbin Mai Magana Da Yawun Shugaban Ƙasa
- Sin Na Maraba Da Masu Zuba Jari Domin Su More Damammakin Bunkasarta
Rundunar ‘yansandan jihar ta ce mutanen na haƙar ma’adinai cikin dare ne lokacin da wajen ya rufta kansu.
‘Yansanda daga ofishin Erena tare da taimakon mazauna yankin sun kai ɗauki, amma sun tarar da sun riga sun rasu.
An kai gawarwakinsu asibitin Zumba.
Rundunar ‘yansandan ta ce ta fara bincike kan lamarin, kuma ta ja kunnen jama’a da su guji irin wannan aiki da ya ke barazana ga rayuka, tsaro da tattalin arziƙin jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp