Tsohon Ministan Matasa da Wasanni, Solomon Dalung, ya ce yawancin ‘yan siyasa da ke sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC mai mulki suna yin hakan ne saboda tsoro, ba don kishin jama’a ba.
Ya faɗi haka ne a ranar Talata yayin wani shiri mai suna The Morning Brief a tashar Channels.
- Binciken Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN: Cin Zali Ta Hanyar Kakaba Haraji Ya Illata Kimar Amurka
- Ƴan Bindiga Sun Kashe Shanu 37 A Filato
Dalung ya mayar da martani ne kan sauya sheƙar Gwamnan Jihar Delta, Sheriff Oborevwori, daga jam’iyyar PDP zuwa APC tare da wasu jiga-jigan PDP a jihar.
Gwamna Oborevwori ‘, ya ce sauya sheƙarsa domin ci gaban jihar Delta ne, amma Dalung ya ce hakan ba gaskiya ba ne.
Ya bayyana sauya sheƙar a matsayin wata hanya da wasu ‘yan siyasa ke bi don gujewa hukunci ko neman kariya daga matsaloli.
Dalung, ya ce wannan sauyin jam’iyya ba yana nufin suna da wata aƙida ko kishin ƙasa ba, illa kawai don kare kai da ci gaba da riƙe madafun iko.
Ya ƙara da cewa, kamata ya yi al’umma su kasance masu yanke hukunci kan ko sauya sheƙar ya dace ko bai dace ba, ba wai ‘yan siyasar da kansu ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp