Gwamnatin Sojin Nijar ta soke yarjejeniyar da ta ƙulla da ƙasashen Rasha da Turkiyya dangane da tattara bayanan sirri da fasahar tsaro.
Wannan mataki na zuwa ne bayan rahoton cewa ba ta gamsu da ingancin fasahar da ƙwarewar dabarun aikin da waɗannan ƙasashe ke bayarwa ba.
- EFCC Ta Kama Matashi A Kaduna Bisa Zargin Wulaƙanta Naira A Bidiyon Barkwanci
- Dalilin Da Ya Sa Ɗan Sanda Ya Gyara Wa Ganduje Igiyar Takalmi – Hadimi
Rahoton daga shafin LSI-Africa ya bayyana cewa sojojin sun yanke shawarar ficewa daga wannan haɗin gwiwa ne saboda raunin tsarin tsaron bayanan da Rasha da Turkiyya suka samar.
Haka kuma, wata sabuwar yarjejeniya da Nijar ta kusan cimmawa da wani kamfani daga ƙasar Maroko ta rushe bayan da aka gano cewa kamfanin yana da alaƙa da wani kamfanin Faransa, ƙasar da Nijar ta katse hulɗarta da ita tun bayan juyin mulki.
Tun bayan juyin mulkin da Janar Abdirahmane Tchiani ya jagoranta a watan Yulin 2024, Nijar ta fice daga hulɗar soja da ƙasashen Yamma ciki har da Faransa da Amurka, inda ta koma neman taimako daga sabbin ƙawaye kamar Rasha da Turkiyya.
Sai dai, rikice-rikicen cikin gida da matsalolin tsaro da tattalin arziƙi sun sa gwamnatin ke ci gaba da yin gyare-gyare don samar da hanyoyin da za su ba ta kariya da cikakken iko kan harkokin leƙen asiri da tsaro.
Wannan mataki yana iya nuni da cewa Nijar na ƙoƙarin zama mai dogaro da kai a fannin tsaro, ko kuma tana neman ƙawancen da zai fi dacewa da manufofinta na cikin gida da waje.
Duk da haka, ƙwararru na ganin cewa hakan na iya janyo sabon matsin lamba daga ƙasashen duniya da ƙungiyoyin yanki kamar ECOWAS.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp