Kamfanin mai na Nijeriya (NNPCL) ya sanar da rufe matatar mai ta Fatakwal (PHRC) don gudanar da gyare-gyare da kimanta ingancin aiki, wanda zai fara a ranar 24 ga Mayu, 2025.
A wata sanarwa da babban Jami’in sadarwa na NNPCL, Femi Soneye, ya fitar a yau Asabar, ya bayyana cewa wannan shiri ne na yau da kullum don tabbatar da inganci aikin gidan matatar.
- Matatar Dangote Ta Sake Rage Farashin Man Fetur
- Bayan Fara Aikin Matatar Mai Ta Fatakwal, Sai Kuma Me?
NNPCL ta bayyana cewa tana aiki tare da hukumomi kamar hukumar kula da albarkatun Mai ta tsakiya da kuma kasa (NMDPRA) don tabbatar da ingancin aikin gyara.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp