Rundunar ‘yansandan Jihar Kebbi tare da hadin gwiwar sojojin Nijeriya da ‘yan banga a Kebbi, sun dakile harin da ‘yan bindiga suka kai musu, inda suka kashe daya daga cikinsu tare da kwato bindiga kirar AK47 guda daya a Karamar Hukumar Augie da ke Jihar.
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, SP Nafi’u Abubakar ne, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a Birnin Kebbi a ranar Lahadi.
- Masanin Najeriya: Sin Aminiyar Kasashen Afirka Ce A Ko Da Yaushe
- Amurka Mai Satar Mai Daga Kasar Sham
Ya ce rundunar ta samu labarin cewa a ranar Asabar da misalin karfe 3:00 na dare wasu ‘yan bindiga da ke da yawan gaske sun kai farmaki kauyen Tiggi da ke karamar hukumar Augie a jihar.
“Bayan samun rahoton, rundunar ‘yansandan da aka tura yankin tare da hadin gwiwar sojoji da ’yan banga, nan take aka tattaro ‘yan banga inda suka yi artabu da ‘yan bindigar.
“Sakamakon haka, an kashe daya daga cikin ‘yan bindigar kuma da yawa sun tsere da raunukan bindiga. Sannan an kwato bindiga kirar AK 47 guda daya.”
Sanarwar ta kuma ce Kwamishinan ‘yan sanda, Ahmed Magaji-Kontagora, ya jaddada a shirye rundunar ta ke da kuma jajircewarta na tabbatar da tsaron al’ummomin kan iyaka da jihar daga ‘yan bindiga.
“Ya yaba da jajircewa da kwazon da ‘yansanda, sojoji da ‘yan banga suka yi a yunkurinsu na yaki da masu aikata laifuka,” in ji shi.
Sanarwar ta kuma yi kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da ba ‘yansanda da sauran jami’an tsaro hadin kai, domin rage yawaitar laifuka a jihar.