Daya daga cikin ‘yan takarar Jam’iyyar NNPP na kujerar Sanatan Bauchi ta Kudu, Musa Babangida Maijama’a, ya janye aniyarsa ta yin takarar Sanata tare da mara wa Sanata mai ci a wannan mazabar, Sanata Lawan Yahaya Gumau ‘yan awanni bayan jam’iyyar ta gudanar da zaben fitar da gwani a yankin.
Maijama’a ya janye wa Gumau duba da kwarewar da yake da ita na wakiltar mazabar sama da shekaru, yana mai cewa hakan zai kawo hadin kai da ci gaban jam’iyyar a matakin jihar da ma kasa baki daya.
Maijamaa wanda ya shaida matsayar tasa a wata ganawa da ‘yan jarida a ranar Lahadi, ya ce, “Mun tattauna yadda za a samu hadin kai a jam’iyya mu ta NNPP kuma fahimtar junar ita ce ta kawo wannan matakin.
“Mu uku ne muka yanki Fom din tsayawa takara a jam’iyyar, sai naga ya dace mu yi abun da ya kamata ba ma sai an je ga batun zaben fitar da gwani na ba, don haka na janye kuma zamu ci gaba da tuntubar daya dan takarar.” Cewarsa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp