A yau Talata 15 ga wata, ma’aikatar tsaron kasar Sin ta bude taron shugabannin matasa irinsa na farko na dandalin tattaunawar zaman lafiya da tsaro na Sin da Afrika, wanda zai gudana har zuwa ranar 19 ga wata.
Manufar taron wanda zai samu halartar manya da matsakaitan hafsoshin soja kusan 90 daga kasashen Afirka fiye da 40, ita ce kara cimma matsaya, da karfafa hadin kai a fannin zaman lafiya da tsaro, da ba da gudummawa ga gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta Sin da Afirka.
- Bayan Shekaru 6 A Hannun Boko Haram, Wasu Yara Biyu Sun Kuɓuta
- Girman Kai Da Son Zuciya Ba Za Su Sa A Amince Ko Ba Da Hadin Kai Ba
Tsaro wani muhimmin ginshiki ne na ci gaba da tabbatar da walwalar al’umma. Kafin al’umma ta samu walwala ko wadata, ko bunkasar tattalin arziki, sai ta samu tsaro da kwanciyar hankali. Haka kuma duk wani arziki da kasa ke tinkaho da shi, to ba za ta iya cin gajiyarsa ba muddin tana fama da matsaloli na tsaro.
Ba makawa koma bayan tattalin arziki da mawuyacin halin da kasashen Afrika ke fama da su na da alaka mai zurfi da tabarbarewar tsaro da yaki ci yaki cinyewa.
Hakika tunanin kasar Sin abu ne mai matukar burgewa domin ta kan mayar da hankali ne ga neman mafita mai dorewa. Kamar yadda muka sani, matasa, su ne kashin bayan ci gaban kowace al’umma, haka kuma su ne masu tafiya da zamani da ganin irin abubuwan dake faruwa a cikin al’umma. Baya ga haka, su ne za su fi fahimtar yadda bata-gari ke tunani.
Gayyato matasan Afrika da Sin ta yi, yana da muhimmanci ga warware matsalar da kasashensu suke fama da su, kasancewarsu na da kaso mai yawa cikin al’umma, kuma akasari su ne suka fi jin radadin tashe-tashen hankula da yake-yake, don haka yin watsi da ra’ayoyinsu, ba zai taba kawo mafita ga halin rashin tsaro ba. Amma sanya matasa cikin manufofi da dabarun tsaro da na raya kasa, zai kai ga warware tushen matsalolin.
Bugu da kari, tunaninsu ya bambanta da na wadanda suka gabace su, don haka za su iya kirkiro sabbin dabarun samar da mafita da za su kore wadanda aka dade ana amfani da su.
Tabbas ba su dama na tattaunawa da Sin ta yi, ya samar da wata mahanga ta daban, wadda muke sa ran za ta taimaka wajen sauya alkiblar yaki da matsalolin tsaro da za su kawo mafita. Bugu da kari, bisa la’akari da zuwansu, za su koyi darrusa daga kasa mai gogewa kamar Sin, wadda duk da yawan al’ummarta, tabbatar da tsaronsu bai taba gagararta ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp