Wasu ‘yan bindiga sun kai hari ƙauyen Lambo da ke ƙaramar hukumar Kurfi a Jihar Katsina.
A yayin harin sun jikkata mutane biyu tare da sace mutane da dama, ciki har da maza, mata da yara.
- Kwankwaso Ne Kaɗai Ɗan Siyasar Da Zai Iya Maye Gurbin Buhari — Jigo A NNPP
- Kotu Ta Umarci Gwamnatin Bauchi Ta Biya Tsohon Akanta-Janar Naira Miliyan 100
Shaidu sun ce ‘yan bindigar sun zo ne da yawa kuma suka fara harbe-harbe ba tare da ƙaƙƙautawa ba, lamarin da ya sa mazauna ƙauyen suka gudu zuwa dazuka domin tsira da rayukansu.
Rahotanni sun nuna cewa ‘yan bindigar sun riƙa shiga gidaje suna sace mutane, lamarin da ya jefa al’umma cikin firgici da tashin hankali.
Wani masani kan tsaro mai suna Bakatsine ya wallafa a shafinsa na X a ranar Talata cewa: “A daren jiya, ‘yan bindiga sun kai hari ƙauyen Lambo da ke ƙaramar hukumar Kurfi, Jihar Katsina.
“Sun jikkata mutane biyu tare da sace maza, mata da yara da dama.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp