Sa’oi 24 da Fadar Shugaban kasa ta bigi ikirarin cewa, ofishin Malam Nuhu Ribadu a watanni 24 da suka gaba, ya samu nasara kan yakin da ke yi da ‘yan ta’adda da kuma ‘yan bindigan Daji, kwatsam, sai kuma a makwannin da suka wuce, wasu mahara suka kutsa cikin wani Masallaci a garin Malumfashi na jihar Katsina suka kai mummunan hari a yayin da masallatan ke kan tsakiya da gabatar da Sallar Asuba, suka hallaka masallata 30.
Sai dai, abin da ake cewa wai, ihu bayan hari, daga baya jami’an tsaro a garin sun nemi daukin sauran jami’an tsaro domin kai dduki bayan maharan sun kaddamar da harin na su.
- Me Ya Sa Wasu Kafofin Watsa Labarun Japan Suke Kokarin Musanta Kisan Kiyashin Nanjing?
- Ƴansandan Libya Sun Kama Ƴan Nijeriya Biyu Kan Zargin Fashi
Fadar Gwamnatin kasa ta yi ikirarin cewa, Gwamnatin kasar ta gaji matsalar tsaron ne, daga Gwamnatin baya, amma ta yi ikirarin cewa, bisa dabarun da Nuhu ya samar, musamman ta hanyar yi wa tsarin tsaron kasar garambawul, da kuma yin aikin hadaka da sauran hukumomin tsaro, hakan ya sanya ofishin na Nuhu, samun nasara a wanzar da ayyukan tsaro na sirri, tare da kuma yin hadaka da hukumomin tsaro na kasa da kasa, musamman domin a kara karfafa tsaro a cikin kasa.
Ba wai muna yin jayya da sanarar da ofishin Nuhu ya samu a tsakanin wadannan watanni ba ne kuma muna sane da kokarin da yake yi, na ganin cewa, ‘yan Nijeriya na samu su kwanta su yi barcin dare, idanuwansu biyu a rufe ba tare da wata fargabar ko za a kai masu hari ba.
Tabbas, muna jinjina masa kan yunkurin da yake ci gaba da yi na rage kalubalen rashin tsaro da Gwamnatin mai ci ta gada.
Amma mummunan harin da wasu mahara suka kai a watannin baya a yankin Yelwata, inda suka yi wa wasu al’umomin yankin kisan kiyashi da kuma harin da ‘yan bindiga suka kai kan Masallaci a garin Malumfashi ta Jihar Katsina, ba makawa hakan ya nuna cewa, kamar an yi gaggawa kan ga murnar samun nasara ta yakin da ofishin Nuhu ke kan yi, da ‘yan ta’adda da kuma ‘yan bindiga Daji duk da kuwa nasarar kame da kuma kashe wasu kasurguman ‘yan ta’adda da ofishinsa ya yi.
Kazalika, irin wannan salon ikirarin samun nasara a yakin da ‘yan ta’adda ne, Gwamnatin da ta shude ta rinka shelanata cewa, ta samu, amma a zari, batun akwai lauje a cikin nadi.
Domin kuwa, kusan shekaru takwas na Gwamnatin da ta gabata ta yi, kalubalen rashin tsaro ya jefa rayuwarsu, a cikin tasku, duba da yadda ‘yan tayar da kayan baya a kasar suka kusan durkusar da bangaren tsaron kasar, ta hanyar aikata ayyukansu na ta’addacin wanda lamarin ya kai ga har an nuna bukatar a yi wa fannin tsaron garanbawul.
Bugu da kari, ‘yan Nijeriya da dama,, sun ta yin kiraye-kirayen da a dauki mataki kan kalubalen rashin tsaro da ke addabar kasar a zahirance, ba wai kawai yin bayanai, da fatar biki da hukumomin tsaron kasar ke yi na cewa, sun kurmushe kaifin ‘yan ta’addar Kungiyar Boko Haram.
Hakazalika, a tsakanin wadannan watannin, manyan hukumomin tsaro na kasa sun ta yin bayanan zaurance domin nunawa ‘yan kasa tamkar komai na tafiya daidai, bayan alhali a bayan fage, ‘yan ta’adda na ta kai komon, yunkurin durkusar da kasa.
Har zuwa yanzu, ‘yan Nijeriya na ci gaba da zama a cikin kwankwaton ikirarin da hukumomin tsaron kasar ke yi na murkushe kaifin ‘yan Boko Haram inda kuma a zahirance, ake ganin ‘yan gudun hijira a yankin Arewa Maso Gabas ke kara kwarara zuwa sansanonin ‘yan gudun hijira da ke a yankin domin tsira da rayuwarsu.
A gefe daya kuma, manyan hanyoyin kasar sun koma tamar tarkon mutuwa ga matafiya inda ake tare su, a wasu yankuna, a hall aka su.
Masu garkuwa da mutane da sauransu, na ci gaba hana ‘yan Nijeriya sakat saboda ayyukansu da suke ci gaba da gudanarwa.
An dai nada Nuhu Ribadu a mukamin mai bai wa shugaban kasa shawara ne, bisa la’akari da nasarorin da ya samar, a lokacin da ya kasance shi ne shugaba na farko, na hukumar EFCC.
Nuhu tsohon Dansanda ne, wanda ya yi ritaya, a matsayin mataikin Sifeta Janar na ‘Yan Sanda.
Amma idan har zamu yiwa hukumomin tsaron adalaci, za mu iya cewa sun yi kokar wajen kashe ‘yanbindiga da dakile hare-haren ‘yan ta’adda a jihohohi kamar Zamfara, Katsina, Kaduna da Sokoto.
Sai dai, bisa maganar gaskiya, har yanzu za a iya cewa, akwai sauran gagarumin jan aiki, a gaba, game da magance matsalolin rashin tsaro a kasa.
Kalubalen rashin tsaro da ‘yan Nijeriya ke ci gaba da fuskanta matsala ce da ke bukatar yin tunani mai zurfi da bunkasa salon dabarun yaki tare da daukar kwararan matakan da suka kamata, domin a kawo karshenta.
Kamata ya a ce, ofishin Nuhu Ribadu ya zama tamkar cibiyar da za a zauna a wasa kwakwalwar yin nazarin tsara yadda za a tunkari kalubalen rashin tsaron musamman duba da cewa, zuwa kai farmaki fagen daga ba hurumin sa ba ne.
Malam Nuhu Ribadu na da bukatar samun kwararru da za su taimaka masa da kuma shi kan shi tsarin tsaron kasa.
Bugu da kari, batun na samun nasara a yakar ‘yan ta’adda da kuma ‘yan bindiga, ba shi ne abin da a yanzu ‘yan kasa ke bukatar ji ba, domin a namu ra’ayin abin da suke bukata daga gun hukumomin tsaron shi ne, kara jajircewarsu wajen samar da dawamamen zaman lafiya a kasa.
Muna kira ga Malam Nuhu Ribadu da ya yi amfani da karfin ofishinsa wajen kara matsawa dakarun soji da ke a fagen daga na su kara kwazo kan yakin da suke ci gaba da yi da ‘yan ta’adda da kuma ‘yan bindiga.
A namu ra’ayin, nuna ganin kamar an yi riga Malam Masallaci kan batun cewa, an samu nasara kan yakar ‘yan tayar da kayar baya a kasar nan, musamman duba da cewa, har yanzu ‘yan Nijeriya na ci gaba da zama a cikin fargabar hare-haren’yan bindiga da kuma ‘yan ta’adda.
Kazalika, duba da cewa, masallata a Masallatai na gudanar da ibada a cikin jimanin tsoro, wannan babban abin nuna damuwar ne bayan cewar, nauyi ne a kan jami’an tsaro su tabbatar da suna kare rayuka da dukokiyoyin ‘yan kasar .
Rashin imanin da ya aku a jihar Katsina da kuma a yankin Yelwata abune da ya nuna irin gazawar da ake da ita, bangaren samun bayanan sirri. A yayin da muke taya Fadar Shugaban kasa murnat samun wannan nasarar ,amma muna ganin har yanzu akwai sauran jan aiki a gaba kan batun kalubalen rashin tsaro a kasar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp