Gidauniyar Yara ta Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ta bayar da wani rahoto da ya girgiza al’ummar Nijeriya da ma Duniya baki daya.
Rahoton ya bayyana cewa, Nijeriya ta yi asarar fiye da Dala Biliyan 100 a bangaren tattalin arziki a shekara 10 da aka yi ana tafka rikici a yankin Arewa maso Gabashin kasar, yakin da ‘yan ta’addan Boko Haram ke jagoranta.
Tabbas wannan bayanin ya ratsa al’umma Nijeriya ya kuma tayar da bukatar a sake tunani tare da nemo hanyar magance matsalar da ke haifar da wadannan rikice-rikice da suka ki ci suka ki cinyewa.
Rikicin da a halin yanzu ya yi shekaru ana tafkawa, don an fara ne a shekarar 2008 har zuwa lokacin da aka rubuta rahoton wato shekarar 2021, ya bar alamomi na tashin hankali a bangaren zamantakewa da tattalin arzikin Nijeriya gaba daya.
Rahoton ya kuma kara da cewa, an kashe mutum fiye da 35,000 tun da aka fara wannan rikici a shekarar 2009 lokacin da kungiyar Boko Haram ta kaddamar da gwagwarmayarta na hambarar da gwamnatin Nijeriya don kafa tsarin mulkin Musulunci.
Rahoton na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana sakamakon da rikinci ya haifar ga al’umma tun daga rasa rayuka, raunata al’ummna da dama, rasa matsugunai da kuma yadda al’amarin ya shafi tattalin arzikn kasa gaba daya.
Wadannan su suka taru suka nemi durkusar da tattalin arzikin kasa abin da kuma bai kamata a yi banza da shi ko kuma a kawar da kai ba.
Rahoton ya kiyasta asarar da aka yi ga tattalin arzikin kasa da kuma irin yadda al’amarin ya durkusar da kokarin da gwamnatoci suka yi na bunkasaa tattalin arzikin yankin da ma Nijeriya baki daya.
Kiyasin da aka yi na asarar Dala Biliyan 100 yana nuna abubuwan da aka yi asara na wadanda za a iya gani da idanuwa da kuma asarorin da aka yi wasu matakai da ya kamata a dauka amma ba a dauka ba da kuma kubutar da mutane daga talaucin da ba a iya yi ba sakamakon rikice-rikicen.
Matsalolin da rikicin ya haifar bai takaita ga yankin Arewa maso Gabas kawai ba, duk da cewa daga nan ne rikicin ya samo asali, lamarin ya shafi dukkan kasar ne, kamar yadda rahoton ya nuna.
Koma baya da aka samu na tattalin arziki a yankin ya faru ne saboda yadda aka fuskanci rikice-rikicen ba tare da kaukautawa ba, wanda hakan ya shafi zaman lafiyar Nijeriya gaba daya.
A wannan lokaci da duniya ke zaman cude ni in cude ka, matsalolin da Nijeriya ke fuskanta yana iya shafar zaman lafiyan kasashe makabtanmu da ma yankin Afrika gaba daya.
Wakiliyar UNICEF a Nijeriya, Cristian Munduate, ta yi daidai inda ta bayyana cewa, koda an iya murkushe wannan tashin hankali to lallai barnar da tashin hankalin ya haifar zai dade ana ci gaba da jin radadinsa.
A ra’ayinmu in har ana son a yi maganin wannan matsalar, dole Nijeriya ta dauki matakai masu muhimmanci, na farko dole a dauki matakan kawo karshen rikicin tare da dawo da zaman lafiya a yankin Arewa maso Gabas tare da samar da yanayin yafiya a tsakanin al’umma da kuma tsugunar da wadanda yakin ya tarwatsa, ta haka za a samar da fahimtar juna a tsakanin al’umma, wanda kuma hakan zai kai ga samar da dawwamanmen zaman lafiya, sannan ta haka za a iya yin maganin matsalolin da rikicin ya haifar na tsawon shekara fiye da 10.
Bugu da kari kuma, zuba jari a bangaren ilimi da kiwon lafiya yana da matukar muhimmanci musamman ga yaran da rikicin ya raba da iyalansu da kuma gidajensu, haka yana da matukar muhimmanci.
Wannan jari da za a zuba ba wai kawai ya zama dole ba ne yana kuma da matukar muhimmanci a wajen samar da yara masu cikakkiyar lafiya da ilimi, hakan kuma shi ne ginshikin ci gaba da bunkasar kasar baki daya.
Haka kuma yana da muhimmanci a samar da wasu hanyoyin samun kudin shiga ga kasa, dogaro ga bangaren man fetur ba zai haifar da da mai ido ba ga Nijeriya. Dole Nijeriya ta nuna wasu hanyoyin samun kudaden shiga wanda zai samar mana da ci gaba a bangaren samar da ayyukan yi ga matasanmu da rage talauci a tsakanin al’umma.
Baya ga kokarin da ake yi a cikin gida, hadin kai da kungiyoyin kasashe waje yana da matukar muhimmanci. Dole Nijeriya ta nemi gudummawar abokan hulda na kasashen waje wajen neman yadda za a samu saukin kawo karshen rikicin da kuma yadda za a yi maganin abubuwan da rikicin ya haifar. Al’umma na da muradin ganin sun taimaka wa Nijeriya da hanyoyin magance matsalolin tare da samar da zaman lafiya don ta haka za a tabbatar da zaman kafiya a duniya baki daya.
A ra’ayinmu, wannan rahoton yana karfafa bukatar rungumar matakan kariya ne na kokarin kauce wa fadawa irin wannan rikicin a nan gaba. Samar da hanyoyin kare aukuwar rikici zai kai ga ceto rayuwar al’umma da kuma ceto tattalin arzikin kasa. Don haka bayanin cewa, an yi asarar fiye da Dala Biliyan 100 a rikincin yankin Arewa maso Gabas ya kamata ya farkar da mu, kuma hakan ya zama izna ga Nijeriya da ma Duniya baki daya a kan bukatar a rungumi hanyoyin kare aukuwar rikici ba wai sai wani abu ya faru ba a fara kame-kame.