Daga karshe dai gwamnatin tarayya ta saurari kiraye kirayen ‘yan Nijeriya suka yi na neman a bayyana sunayen wadanda ke daukar nauyin ayyukan ta’addanci a fadin kasar nan, abin da ya kamata ta yi shekaru masu yawa da suka wuce. An jirkirta bayyana sunayen wadanda suke daukar nauyin ‘yan ta’adda ne saboda wasu dalilai da suka hada da na siyasa, musamman a lokacin mulkin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari. Shawarar da kasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ta yanke na bayyana sunayen wasu ‘yan Nijeriyan da ke hada baki da su wajen daukar nauyin masu aikata ta’addanci a Nijeriya bai zaburar da gwamnati ba wajen yin abin da ya kamata har sai a makon jiya da Hukumar Kula da Yadda Ake Sarrafa Kudi (NFIU), ta yi bayani, inda ta sanar da cewa, wasu mutane 9 da cibiyoyin canjin kudi 6 suke daukar nauyin ta’addanci a Nijeriya.
A kan haka ne dole a yaba wa Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu saboda karfin halin da ya yi na bayyana sunayen. Haka kuma ya kamata a yaba wa Shugaba Tinubu a kan yadda jami’an tsaro suka gayyaci Sheik Gumi don ya yi masu bayanin abin da ya sani game da yadda ‘yan ta’addar ke gudanar da harkokinsu.
Sanannen Malamin addinin musuluncin nan mazaunin jihar Kaduna dakta Ahmad Gumi yana kan gaba na kira da a rika tattaunawa da ‘yan ta’addar don ganin sun sako wadanda suka yi garkuwa da su, ya nuna rashin amincewarsa a kan yadda gwamnati ke amfani da karfi a kan ‘yan bindiga, inda ya yi gargadin al’amurra na iya tabarbarewa in har ba a yi abin da ya kamata ba.
- Kasar Sin Na Bayar Da Cikakken Goyon-Baya Ga Pakistan Wajen Yakar Ta’addanci
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 5, Sun Saki 51 Bayan Biyan Fansa A Kaduna
Ita kuwa hukuma, a takardar sanarwar da ta fito da ita a ranar 18 ga watan Maris 2024 ta bayyana sunayen wasu kamfanonin canjin kudi da wasu mutane masu zaman kansu da ke daukar nauyin ayyukan ta’addanci a Nijeriya inda ta ba da shawarar a dauki matakin hukunci a kan su ba tare da bata wani lokaci ba.
Cikin wadanda aka sanar da sunayensu, wanda ya fi yin fice daga ciki shi ne mawallafin nan na Kaduna, Tukur Mamu, sunan shi yana cikin jerin masu daukar nauyin ta’addancin ne saboda yadda ya jagoranci karbar kudaden da suka kai Dala 200,000 na kudin fansa a kan mutanen da aka sace a kan jirgin kasan nan da ya taso daga Abuja zuwa Kaduna wadanda ‘yan ta’addar ISWAP suka sace. Idan za a iya tunawa a halin yanzu gwamnati ta gurfanar da Mamu a gaban kotu a kan laifin tallafa wa ‘yan ta’addar a harin da suka kai wa jirgin da ya taso daga Abuja zuwa Kaduna watan Maris na shekarar 2022.
Bayan kasancewar su mambobi a wasu manya-manyan kungiyoyin ‘yan ta’adda na duniya wadanda aka bayyana sunayen su sun kasance cikin wadanda ake zargi da hannu a hare-haren ta’addanci da aka kai Cocin St. Francis Catholic Church na garin Owo,Jihar Ondo a ranar 5 ga watan Yuni na shekarar 2022 da wanda aka kai gidan yarin Kuje da ke Abuja a ranar 5 ga watan Yuli 2022.
Amma kuma abin lura a nan shi ne al’ummar Nijeriya basu nuna zakuwa ba da jin dadin bayanin da aka yi na bayyana sunayen masu daukar ayyukan ta’addanci, wannan kuma ya faru ne saboda a baya an sha kama manya-manyan masu garkuwa da mutane amma sai ta kasance iyakar labarin Kenan.
Alal misali a shekarar 2022, gwamnatin tarayya ta sanar da kasancewar kungiyoyi 96 da suke ayyukan tallafa wa ‘yan ta’addar Boko a kasar nan. Ministan yada labarai na wancan lokacin ya bayyana wa duniya a wani taron manema labaran da ya kira a Abuja inda ya ce, gwamnati ta gano kamfanoni 123 da cibiyoyin canji 33 da aka tabbatar da suna taimaka wa ‘yan ta’addar. An kuma kama masu garkuwa da mutane 26 da masu taimaka musu mutum 7.
Bugu da kari Ministan ya ce, an kama mutum 45 da suke daukar nauyin ta’addanci,kuma za a gaggauta hukunta su amma ba mu sake jin wani bayani a kan lamarin ba sai a wannan lokacin kuma ba mu ji an hukunta wani ko wata ba har zuwa wannan lokacin.
A shekarar ne kuma gwamnati ta kara fadada aikin binciko da sa ido a kan masu daukar nauyin ta’addanci inda ajka bayar da umarnin sa ido don gano yadda kudi ke zirga-zirga a tsakanin ‘yan ta’adda da masu daukar nauyin su.
A ra’ayinmu bai kamata a zargi wannan gwamnatin ba a kan mastalolin da ta gada shekara da shekaru, musamman ma ganin lamarin ayyukan ta’addanci ya dade a kasa ya kuma samu wuri ya zauna a yankuna daban-daban na kasar nan.Abu ne da yake bukatar kowa ya bayar da tasa gudummawar don ganin an samu nasarar yaki da dukkan nau’oin ta’addanci.
A kan haka ne ya zama dole ga wannan gwamnati ta tsaya wajen ganin an hukunta dukkan wadanda aka samu da hannu a daukar nauyin ta’addancin, ta haka ne za a iya tabbatar da cewa, lallai gwamnatin da gaske take yi.Haka kuma ya kamata dukkan rundunonin tsaronmu su hada kai tare da aiki tare.Ana kuma bukatar ‘yan Nijeriya su taimaka wajen bayar da bayanan sirri da za su kai ga sa an bankado ayyukan masu garkuwa da mutane a duk inda suke a fadin tarayyar kasar nan.