Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC), ta yi Allah wadai da sabon karin farashin man fetur da aka yi a fadin kasar.
Sabon karin farashin ya haura Naira 1,000 kan kowace lita a gidajen mai, wanda hakan ke kara barazanar jefa ‘yan Nijeriya cikin kangin talauci.
- Kasar Sin: Ba Makamai Da Takunkumai Ake Bukata Wajen Warware Rikicin Palasdinu Da Isra’ila Ba
- Firaministan Kasar Sin Zai Halarci Jerin Taruka Tare Da Ziyartar Laos Da Vietnam
Shugaban NLC, Kwamared Joe Ajaero, ya zargi Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPCL) da yin karfa-karfa a harkar man fetur.
Ya ce kamfanin yana taka rawa fiye da yadda ya kamata, wanda hakan ke durkusar da harkokin kasuwanci.
Ajaero ya bukaci gwamnatin tarayya ta samar da cikakken tsarin bunkasa tattalin arziki maimakon yin amfani da hanyoyin wucin gadi.
NLC ta yi gargadin cewa karin farashin zai kara talauta ‘yan kasa, rage yawan masana’antu da kuma jawo karin yawan marasa aikin yi.
Kungiyar ta kuma bukaci gwamnatin ta bayyana manufofinta na tattalin arziki a fili maimakon zartar da matakai na ba-zata da ke kara jefa ‘yan kasa cikin wahala.