Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya ce zai janye tsofaffin takardun kudin Naira a hankali tare da maye gurbinsu da sabbi.
Mukaddashin gwamnan CBN, Folashodun Shonubi, ne ya bayyana hakan a ranar Talata bayan taron kwamitin kula da harkokin kudi na bankin (MPC) a Abuja.
- NLC Ta Bai Wa Tinubu Kwanaki 7 Don Dawo Da Tallafin Mai, Ko Ta Shiga Yajin Aiki
- Jami’an Tsaro Sun Tsare Shugaban Nijar Kan Fargabar Yunkurin Juyin Mulki
“Idan aka buga kudi kuma aka fitar da su ana sa ran za a yi amfani da su har zuwa lokacin da za su tsufa kuma har lokacin da babban banki zai janye su ya meye gurbinsu da sababbi, abin da muke yi ke nan”, a cewarsa.
“Dole ne mu fitar da tsofaffin takardun kudi. Kuma yayin da suke shigowa, ana sarrafa su kuma ana dawo mana da su sannan mu kuma mu sake fitar da su domin maye gurbin tsofaffin da sababbi.”
A watan Oktoban shekarar da ta gabata ne, Gwamnan CBN Godwin Emefiele wanda aka dakatar, ya bullo da shirin sake fasalin takardun kudi na N200,N500 da kuma N1000.
Sai dai sauya fasalin kudin ya bar baya da kura da kuma haifar da cece-kuce, lamarin da ya sanya gwamnatin APC ke ganin makarkashiya aka shirya mata don faduwa zaben 2023 da ya gudana.