A Karon Farko Kasar Sin Ta Zama Kasa Mafi Shigo Da Koffi Daga Habasha

Daga CRI Hausa,

Kasar Habasha ta samu kudin shigar da ya kai dala miliyan 578 daga cinikin koffi da ta fitar zuwa ketare a cikin watanni shida da suka gabata, lamarin da ya nuna cewa a karon farko kasar Sin ta kasance a matsayin kasa mafi shigo da koffi daga kasar Habasha. Hukumar gudanarwar koffi da ganyen shayi ta kasar Habasha ta sanar da hakan a ranar 20 ga watan Janairu.

A shekarun baya bayan nan, koffin kasar Habasha yana samun karin karbuwa daga masaya Sinawa.

A ranar 19 ga watan Janairu, jakadan kasar Habasha a kasar Sin, Teshome Toga Chanaka ya ziyarci dandalin kasuwanci na zamani da aka watsa kai tsaye a kasar Sin, kuma an yi cinikin fakiti 10,000 na koffi din kasar Habasha a cikin dakika biyar, lamarin da ya kara bunkasa huldar cinikayyar kayan amfanin gona a tsakanin Sin da Habasha. (Ahmad Fagam)

Exit mobile version