Connect with us

LABARAI

A Sabon Hari A Katsina: ‘Yan Bindiga Sun Kashe Maigarin Garin Mazoji

Published

on

Sama da mahara Hamsin ne ayau Asabar suka zagaye Kauyen Mazoji dake Karamar Hukumar Matazu, a yayinda Maharan suka kashe Sarkin garin.
Wannan ya biyo bayan wasu hari da aka Kai a garin Yantumaki dake Karamar hukumar Danmusa, kuma hakan ya jawo Mutuwar Hakimin garin Mai suna Alhaji Mai Dabino.
Wanda ya bada labarin, ya fada cewa maharan sunkai harin ne a garin na Mazoji da misalin karfe biyu na dare a yadda suka shafe sa’o’I suna cikin garin kafin sukashe sarkin garin.
Maharan dai an fada cewa sun kona mashina guda biyar a yadda ba’asan yawan shanun dasuka bata ba.
Ya kara da cewa yayi matukar bakin ciki akan yadda har yanzu 7:30am amma babu wasu jami’an tsaro dasuka zo garin
Ta’addanci da garkuwa da mutane dai ya zama ruwan dare a ‘yan kwanakin nan a Jihar ta Katsina yadda yabar wasu da dama sun rigamu gidan gaskiya wasu kuma sun bata-bat.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: