Birni ne da ya hada kasar Indiya da tekun Fasha, Lebant da kuma Nahiyar Turai, Al’Ula birni ne da ya tara al’ummomi daban-daban wadanda suka suffantu irin dabi’un mazauna garin.
A yau wannan birni mai ban sha’awa ya zama wata cibiyar yawon bude ido a duniya ga kasar Saudiyya, kyakkyawar manufa, kayatar da baki, da taskokin kayan tarihi, alkinta wurare masu kayatarwa da tare da manufofin hangen nesa.
Al-‘Ula ya samo asali a tarihi na dubban shekaru, tare da matsugunan mutane a yankin tun daga shekara ta 5000 BCE a lokacin Bronze Age.
Da fari ya samu bunkasa ta hanyar dabarun kasuwanci, da wadatattun hanyoyi don jigilar kayan alatu kamar kayan dandano, siliki, da turare a fadin duniya. Hanyar da ta hadu da yankuna masu nisa da suka hada Masarautar Aksum a Afirka, Larabawa, Masar, da Indiya, wanda hakan ya sa ta zama wata mahadar ‘yan kasuwa.
Ilimin kimiyya na nuni da cewa daga yankin an samu abubuwa da dama na game da wayewa.
Kazalika Birnin Al-‘Ula ya taba zama wani bangare na tsohuwar Masarautar Dedan, inda daga baya kuma, ya zama Masarautar Lihyanite, wadanda dukansu suka bunkasa a karni na farko BCE.
Birnin yana nuna tasirin kabilar Larabawa makiyaya Nabataeans, wadanda suka yi fice wajen samun nasarori a fannin gine-gine, da aka fi sani da Petra. Al’Ula ya zama cibiyar al’adu da tattalin arziki a yankin, wanda ya hada alaka tsakanin kasashen Larabawa da yankin tekun Bahar Rum.
Daya daga cikin shahararrun wuraren tarihi na birnin shi ne Hegra, wanda aka sani da Mada’in Saliḥ. Wannan wurin binciken kayan tarihi ne wanda ke da tazarar kilomita 22 daga Arewacin Al-‘Ula, sannan shi ne wuri na farko a kasar Saudiyya da Majalisar Dinkin Duniya ta amince da shi a matsayin wurin tarihi na UNESCO.
Nabataeans ne suka gina birnin sama da shekaru 2,000 da suka gabata, kuma ana ambaton Hegra da “sister city” wato birnin ‘yar’uwa ga Petra. Kamar dai Petra, Hegra wani daki ne da manyan mutum-mutumin ke ciki wadanda aka sassaka su da dutse da wasu sauran gine-ginen da aka kawata su kuma ake basu kulawa na tsawon karnuka. Wurin, a halin yanzu ya zama wuararen kai ziyara ga masu yawon bude ido bayan samun cikakkiyar kulawa, yana sanya wa masu yawon bude idanu da sanin irin ci gaban Nabataean suka samu.
Birnin Al-‘Ula mai katanga, da aka fi sani da Al-DÄ«rah, har yanzu yana nan a matsayin abin tunawa wanda shi ne asalin tushen garin, yana kewaye da tarin tulunan laka da gidaje na dutse, gine-ginen tarihi dake birnin yana nuni dabarun rayuwar mazaunansa, wadanda suka dace da rayuwa a cikin hamada ta hanyar amfani da albarkatun yankin cikin hikima.
Tarihin matsugunin yana na alamta bunkasar mulki a tsakanin dauloli daban-daban. An ambaci daular Dedanite, wadda ta mallaki wannan yanki a karni na 7 da 6 BCE, a cikin tsoffin matanin rubutu kamar Harran Stela, takardar da ta kwatanta cin nasarar Nabonidus, wanda shi ne shugaban karshe na Daular Babila.
A shekara ta 552 BCE, Nabonidus ya kaddamar da yakin soji zuwa Arewacin Larabawa, ya kame manyan birane kamar Tayma, Dedan, da Yasriiba wato (Madina a yanzu).
Bayan faduwar daular Dedaniyawa, Lihyanawa sun karbe ikon Al-Ula inda suka ci gaba mulkin yankin har wajen karni na 5 BCE. Daular Lihyanawa ta kai kusan karni hudu har sai da Nabataean suma suka karbe yankin. Daga karshe Daular Roma ta ci Nabataeans da yaki wadda ta samu nasarar mamaye yankin zuwa lardin Arabiya Petraea a shekara ta 106 CE, ta kara hade Al’Ula inda ta koma karkashin mu’amalarsu, al’adu da tattalin arziki na kasashen Greco-Romawa.
Al-Ula ya ci gaba da taka muhimmiyar rawa a farkon bayyanar Musulunci. Yayin da daular Musulunci ta fadada, sai birnin ya zama wani yanki na Hejaz, yanki mai muhimmanci a farkon tarihin Musulunci.
A karni na 7, yankin tekun ya sake bunkasa a matsayin cibiyar kasuwanci karkashin Daular Banu Umayyawa da Banul Abbas.
Al-Mabiyat, wani kauyen da ke kusa da shi wanda ya bunkasa tun daga karni na 7 zuwa na 13, ya zama wata muhimmiyar cibiyar kasuwanci. Duk da haka, a karshe sulhun ya gagara, sannan zuwa karni na 13, an gina birnin Al-‘Ula ginin katangar zamani ta hanyar amfani da duwatsu domin kaucewa rugujewar gine-ginen Dedanites da na Lihyanites.
Birnin ya sake samun tagomashi a farkon karni na 20 lokacin da Daular Usmaniyya ta gina hanyar jirgin kasa ta Hejaz, wadda ta hada Damascus da Madina.
A yau, an san Al-‘Ula a matsayin daya daga cikin mafi kyawun yanki na ilimin kimiyya na kayan tarihi a Saudi Arabiya, tare da dimbin rubuce-rubucen da zane-zane da suka watsu ko’ina cikin tsaunin dutse da sahara.
Dutsen Ikma da Ar-Ruzeikiyya wurare ne guda biyu masu mahimmanci na fasahar dutse, wadanda ke dauke da zane-zanen da ke nuni da wuraren farauta, mutane, dabbobi, da abubuwan ban mamaki.
Wadannan zane-zane suna ba da haske game da imani da rayuwar yau da kullum na tsoffin mazauna yankin.
Abubuwan dake kewaye da Al-‘Ula, wanda ke tattare da kwazazzabai masu ban mamaki, kwaruruka, da sifofin duwatsu, suma suna kara kawata yankin.
Daya daga cikin fitattun alamomin su ne Jabal Al Fil (Dutsen Giwa), wani babban dutse da ya yi kama da giwa, wanda ya zama mai kayatar da masu ziyara.
A cikin ‘yan shekarun nan, Al-‘Ula ya sami gagarumin ci gaba da sauyi. A cikin 1980s, birnin ya fara zama na zamani tare da sababbin ci gaba a fannin noma da birane, yana jawo mazauna daga ko’ina cikin yankin, ciki har da makiyaya da ma’aikata bakin haure. Gwamnatin Saudiyya ta hannun hukumar masarautar Al-Ula ta kaddamar da wani gagarumin shiri na raya birnin domin ya zama wurin yawon bude ido da al’adu na duniya.
A shekarar 2018 ne kasar Saudiyya ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya ta tsawon shekaru 10 da kasar Faransa domin hada kai kan ci gaban birnin, wannan hadin gwiwar yana nufin kafa otal-otal na alatu, abubuwan more rayuwa na zamani, da gidan kayan tarihi na duniya wanda zai yi bikin fasaha da al’adun yankin.
Hukumar Masarautar ta kuma kaddamar da wani hadadden bincike na kayan tarihin Al-Ula, tare da tabbatar da cewa an adana wuraren tarihi ga jama’a.
An rufe shafuka da yawa, ciki har da Hegra, don kiyayewa amma an sake bude su a cikin 2020 a zaman wani bangare na manyan dabarun yawon shakatawa na yankin.
Babban abin da shirin ci gaban ya mayar da hankali a kai shi ne dorewa da ci gaban kanana da matsakaitan masana’antu (SMEs) a fannin yawon shakatawa.
Hukumar Masarauta, tare da hadin gwiwar AstroLabs, sun kasance suna gudanar da shirin habaka SME da nufin habaka kasuwancin gida da habaka yanayin yawon shakatawa a Al-‘Ula.
Wannan shiri dai ya yi dai-dai da shirin kasar Saudiyya na shekarar 2030, na neman habaka tattalin arziki da kuma rage dogaro da kudaden shigar da ake samu daga mai.
Ana hasashen Al-‘Ula zai jawo masu yawon bude ido miliyan biyu a duk shekara kuma zai ba da gudummawar Riyal Na Saudiya biliyan 120 ga kudaden hada-hada a kasar nan da shekarar 2030, tare da saukake hanyoyin biza ga matafiya na kasashen duniya.
Daga cikin abubuwan da jawo masu ziyara zuwa wuraren tarihin, akwai Titin Oasis Heritage Trail, Dadan, Jabal Ikmah, da Tsohon Garin Al-‘Ula.
Abubuwan da ake shiryawa game da wannan birni na Al-Ula na gaba ba za su gushe daga dadaddun abubuwan da suka gabata. A maimakon haka, kasar na neman daukaka da kuma da bikin tarihin birnin da ya dade ana mai da shi wata fitilar musayar al’adu da kuma wata alama ta yunkurin Saudiyya na ganin an sabunta shi.
A yunkurin sabunta tsofaffi da sababbin abubuwa, Al-‘Ula an tsara shi don ya zama bbban birnin shakatawa a duniya, da zai ba da hadakar tarihi, al’adu, da yanayi. Gari ne da ya samar da abin da ya gabata da wanda zai zo nan gaba, da ke gayyatar duniya don sake gano abubuwan al’ajabi na tsibirin Larabawa.